kinsan Allah nazia idan
baki wuce muka tafi ba zan babbalaki yanzu nan, ko kallonsa banyiba, na kauda
kaina gefe, yaga da gaske nake yakaimin duka, ko in kauce na tsaya qiqam mugun
halin ya mosta hakan ya qara bashi haushi, dama shima gwanine a gun xuciya amma
dai bai kaini ba, ya fara dukana har na fadi yasa qafa yayi ball dani, hankakin
Inna ya tashi tasan idan zai kasheni a gurinnan ba tashi zanyiba, kuma tunda
nace bazan jeba ba tafiyar zanyiba, tazo ta janye yaya hafeez daga gareni, ba
halin ta mishi fada yanda taga ya chanza har fuskarshi tayi jaa dan tsananin
fushi ,da yake shi yaya hafeez fari ne Sosai ko kunya yaji sai kaga yayi ja,
haka lokacin sanyi ma jaa yakeyi, uwa uba idan yayi fushi sai yayi jaa kamar
bature haka yake, tayi gefe dashi ta daura hannunta akan kafadar shi ta dama,
haba yaya!! Ya zaka biyewa nazia? Yarinyar da ba hankali ya ishetaba, kuma sam
batasan ciwon kantaba, wuce ka shiga mota bari in daukota, yayi mini wani mugun
kallo, rai a bace ya shiga mota yana huci "nima dai m. jabo da nake biye
dasu ya bani tsoro dan nayi niyyar in gudu sai mun hadu birni amma dai nayi ta
maxa na tsaya" inna tazo ta durqusa kusa dani, tace ba tafiya mukayiba
kinsan haryar qaramace shine sai yayanki yace bari muyi kwana kamin kizo shi
yasa baki hango muba kuma ke gashi bakya kallon hanya kina zuwa baki ganmu ba
maimakon ki duba gefenki sai kawai kika nemi guri kika zauna kika fara kuka,
abin ya bani haushi ne dan kada yayanki yace na goyi bayan ki shi yasa nima na
dakeke amma nima raina baiso ba....!! haba autan inna kuka ba naki bane kinga
kin bata wa yayanki lokaci kusan awa biyu fa muna jiran ki kuma ya gayamana
yanada aiki kuma duk ke kika janyo araina naji dadi ko banza na bata masa
Lokaci, amma kuma naji jiki, Lallai nice banida gaskiya sabida ina zuwa kawai
banga motaba sai na zauna na fara kuka, kuma ni kaina nasan ba yanda za'ayi su
tafi su barni, wauta ce take damuna ko qauyanci? na bude baki cike da yawu da
jini na zubar da yawun gefen inna, inna da taga jini hankalinta ya qara tashi,
maimakon in sassauto in lallaba in tashi mutafi sai na fuske, ina sheshe kar
kuka nace inna ba inda zani na fasa tafiya,birnin banza, dan yaga inason inje
birni ne shi isa yake min wulaqanci, yanxu kuma na fasa zuwa asaukemin kayana,
ashe yaya yana jina, da qarfi ya fito motar ya bude bayan motar motar ya
ciromin kayana ya jefini dasu kikaji jakar timmn akaina, tabbas wannan yafi
dukan da yamin qonan rai, inna ta kalleshi, ta daure fuska, ashe bakada
hankali? Mi kayi kenan? To sai ka fito min da nawa kayan nima ba zaniba, tunda
abin naku rainin hankaline, hankalin yaya ya tashi, nima dai naji tsoro kuma
naji kunya, ya durqusa inna.... kamin shiru ka fito min da kayana nace ba zaniba
ko dolene,!! Narasa yanda zanyi akaina ake mishi fada kuma nice banida gaskiya
ga uban taurin kai, ya juyo gurina nazia dan Allah kiyi haquri�� na
sunkuyar dakai, banji dadin abinda na masa ba...
Itama inna taga rashin dacewar hakan abu ya hade masa biyu ta
miqe tsaye ke nazia tashi ki shiga mota kaima wuce mu tafi sumui sumui kamar
munafuka na miqe zan dauki jakar kayana yaya ya karba inna tace sake mata
kayanta ta dauka da kanta, Lallai ban kyautaba kuma duk ni na janyo amma......
Title :
Asshe Kaine Mijina Part 2
Description : kinsan Allah nazia idan baki wuce muka tafi ba zan babbalaki yanzu nan, ko kallonsa banyiba, na kauda kaina gefe, yaga da gaske nake yakai...
Rating :
5