Ya juya mata baya, yafara
da cewa ranar assabar na dawo daga kasuwa sai naga kamar kina neman taxi, sai
na tsaya in rage miki hanya dan unguwar nasan ba'acika samun taxiba, abinda ya
bani mamaki yanda idonki ya rufe kika kasa banbance motana da taxi, dan ni ba
dan taxi bane,har kina gayamin address dinki, bawai nagane bane nayi niyyar
idan naje unguwar naku sai ki nuna mini guri in saukeki... bayan mun isa
unguwarku na miki magana nace mun kawo naji shiru ina ta magana kikayi shiru
nadauka qyaleni kikayi nayi magana har na gaji sai kawai najuya kan motana na
wuce gida nakai saqon baba....
Mun kama hanyar gidana in
dauko wani abu bayan na iso nan sai na qara miki magana shiru,ba motsi na
tabaki naji bakya nunfashi, hankalina ya tashi matuqa, tsoro da fargabar idan
kin mutu yaxanyi dake ya kamani..!!! a haka na daukokoki na kawo ki dakina
batare da na bari kowa ya ganki ba, dama ni Dr ne, na miki treatment, na qara
miki ruwa har zuwa lokacin da kika farfado kika fara xagina,to kinji ataqaice
yanda akayi na samoki, ni banida alaqa da wata sister khadee hasalima ko sunan
ban tabajiba, kuma xan gaya miki Gaskiyar magana sonki nakeyi,taji wani
dummm... aranta tace idan dai xaka kaini gida mai sauqi ne, ya qara mata bayanin
hilinda ya sami kanshi dazu na ganinta da yayi, kuma ya nuna mata cameran da
yake ganinta idan zai kawo mata abinci dan bayason ganinta, tun ranar da ta
mareshi kuma yayi alqawarin horata har na kwana bakwai yama yi nufin keta mata
mutunchi Allahne ya kareta sai kuma Allah ya taimaketa, nan itama tabashi
haquri rashin kunyar da ta mar da taimakon da ya mata, takuma hadamai da
labarin abinda ya faru daga farko har qarshe, yayi mamakin irin zuciyanta da
kuma yanda take iya dukan namiji, yaga marin da tayiwa unlce din sista khadee
ne ya janyo mata haka, dadewar da tayi anan ma sanadin marin da ta mishine,
yanxu dai
Ki shirya inkaiki gurin
inna, wani sanyi naji araina,nayi tsalle da ihu, inata dariya murna...,tace ai
ashirye nake, ya juyo ya kalleni karo na farko daya kalleni tunda ya shigo
dakinnan, kin cire mini tufafina? Eh yanzu zan cire, shine kike cewa kin
shirya? Murmushin da tayi ya qara daga mishi hankali, yasa kai idan kin shirya
ina waje ki fito muje, yana fita na cire kayanshi na maida wayanda ya siyomin
koda sunyi datti amma su na saka hakanan nafito na sameshi, abin mamaki gidan
da nake qaton qaskene kuma part part ne ga mutane a ciki suna kai da kawo, a
raina nace dana sani da na riqa dukan qofa tun Lokacin ai da xa'a jiyoni a bude
min da yanzu na tsufa gida.
Mun isa unguwar mu da
misalin qarfe tara dare, na rangada sallama inna tana ganina ta fara salati Sai
kawai ta fashe da kuka nima na fashe da kuka, tana kuka ina inayi tayi wa yaya
waya ko minti biyar ba'ayiba ya iso, yana zuwa naje na rungumeshi ina kuka,
araina nace ni ban rameba su suka rame, duk sai suka qara bani tausayi, nan aka
fara tambayar ya akayi? Na koro musu bayani daga farko har qarshe, sun
tausayamin kuma mamaki ya kama su, suka gayamin rashin mutuncin da sista khadee
ta musu, anan dai wanda ya kawoni shima yayi bayani nashi, sai dai yayi qarya
sabida ce musu yayi sai jiya da dare na farfado kuma yace tsoro yaji ganin
lalacewar qasa kada yakaini gurin yan sanda ya janyo wa kanshi wani abin daban,
to hakadai a ka jajantawa juna akayi waya qauye aka sanar dasu an ganni iyayen
nura sunji dadi Sosai inna tace gobe sai ayi sadaka......