suma nayi mi nayi Allah masani,
sai farkawa nayi na ganni a wani makeken gado an saka min ruwa, na bude ido a
hankali, na jujjuyasu bansan inane nan ba, nayi qoqarin tashi amma nakasa tashi
kaina yayi nauyi, naduba sai naga ashe ruwa ake qaramin, iya tunanina gidan su
sista khadee ne tunda daga chan nafito, my be faduwa nayi aka maidani chan.!
Kawai sai na daure fuska dan kuwa banason ganinsu. Banason taimakonsu, banason
duk wani abu daya shafesu, ina kwance sai ga wani saurayi gajere fari ya shigo,
ina ganinsa, na fara surutai, miyasa kuka maidani gidanku, miya dameku da
lafiyata da ciwona?? Kumaidani gaidanmu banason ganinku ko kadan, haka nayita
surutai ina qoqarin cire drop dinda aka sakamin sai naji ya riqe hannuna, na
daga ido na kalleshi baice min komai ba saima bina da ido da yayi ina balaee
na, naso in ci gaba sai kuma na fasa sabida kaina yayi nauyi Sosai ihun da
nayi.. namaida kaina, na rufe idona, bacci mai nauyi ya qara daukeni banfarka
ba sai tsakiyar dare, abin mamaki gajerin qaton da na gani daxu shine na gani
kwance a gefena yana sharar bacci abinshi, dayake qadon qatone Sosai, kuSan
gadon ya cika dakin, har yasa ko gurin sallah babu, na tashi ina dube dube ga
dukkan alama nan dakin mazane, amma sista khade ta cuceni maimakon ta kaini
dakinta sai ta ijiyeni anan? Dakin uncle dinta Wallahi nida ita har abada ta
xubar min da mutunci yanxu idan yaya da inna suka ji na kwana daki daya da qato
mi xasu kalleni,.....!!??
N qare tunane tunane da
bala'eena cikin xuciya, nayi niyyar in tayar dashi ya kaini gida amma kuma na
fasa, na dago kaina na hango qofa biyu naje a hankali na murda daya najita gam
a kulle na murda ta gefenta sai ta bude na leqa sai naga ashe toilet ne, ko
nayi wanka bnida tufafin sakawa gwanda in haqura nayi fitsari nafito, raina duk
a bace, ina dubawa naga ledar DAY TO DAY, kuma ledar ta clothes ce sai na buda
ina dubawa naga tufafi da brush da duk abin buqatar mace hadda pad ko sista
khadee dan uban tace mishi bana sallah ohon mata!!!??
Na dauki ledar na shiga
bayi na kulle nayi wanka da yake kaina adaure yake, amma dai gashina anyi sama
dashi hakan ya bani damar wanke gashina tsab, nayi wanka kamar ban taba
wankaba, ga ruwan da zafi Sosai, duk sanyi da kasalar da suka rage naji sun
tafi, nayi brush, amma yunwa ta addabeni, na saka kayan top ne da jeans, nafito
kamar baniba, amma zuciyata cike da haushin su sista khadee, ina fitowa naji
ana kiran sallah, na tuna inna tace kada inkai maqreeb, naje na tayarda wannan
gajeren yana wani mutsuke ido, mlm ka tashi kaje ka kira sista khade akaini
gidan mu ko a budemin qofa inje gida... na fada cike da qadara, wani kallo
yakemin, kallon baisan alqiblar maganataba, kallon mi kike nufi??, ya tashi
zaune, amma kya bari gari ya waye sannan akaiki gida ko,?? wane gari zan bari
ya waye? Yace Bakiji ana sallar asuba bane??Asuba!?? Dama asubace ba maqreeb
ba?? Kuka ya kubucemini ba tare da nasaniba, miyasa sista khadee tamun hakane?
Miyasa zata bari ihar in kwana gidansu kuma ta ijiyeni a dakin uncle dinta??
Lallai khadija ba qawar
kirki bace, wannan duk araina nakeyi, na dago na kalli mutumin nan,na rasa irin
rashin kunyar da xan surfa mai, kawai, nace uncle to sista khadee ta gayawa
inna da yaya ina gidansune??, sabida inna tace kada in kai maqreeb gashi har
gari ya kusa wayewa?? Yayi kasake yana kallona, kayi magana mana uncle, yaji
dadin sunan data kirashi dashi, har yana maimaitawa a fili uncle.!!! amma kuma
shi wacce sista khadee ce take fada haka, Lallai idan yagaya mata baisan sista
khadee ba wannan rudaddiyar zata daga mishi hankali fiye da na yanxu, amma zai
lallabata har gari ya waye sai ya mata bayanin komai, da sanyin murya yace ki
zauna in miki bayani, kinji sister na, da jajayen idona na dago na kalleshi jin
ya fadi sunan da yaya yake kirana dashi, sai na sami kaina ina maibin
umurninsa, na zauna girmn kai ba nawa bane..
Na zauna, kiyi haquri zuwa wayewar gari zan gaya miki komai, kinji? na daga kai
alamar shkenan ba komai, na zauna jigun, chan natuna banyi sallar ko azzahar
bare magreeb gashi har an kira asuba, na miqe naje na dauro alwula nazo nayi
sallolin da suka hau kaina bayan na kammala nayi sallar asuba nayi addu'a Allah
ya fitar dani wannan qangi da sista khadee ta jefani, ya tsareni da sharrin
uncle dinta,!
Anan zaune bacci yayi awon
gaba dani ban farkaba sai guraren tara na safee, ina farkawa na duba bashi ba
labarinshi, na tashi na murda qofa najita kulle gam, ga BF nan an hadamini an
ijiye mini, wasu zafafan hawaye suka gangaro a kumatuna Lallai sista khadee ta
cika yar iska! Wato haka zata min ko? Ba wata mafita illa in danne abincina in
barwa Allah ko na mutu in tafi ciki da nauyi.!!
A bangaren iyayen nazia
kuwa tunda inna taga an kira maqreeb bata dawo ba ta kira wayar nazia, tana
ringing amma ba'adauka, tayi ta kira har ta qufula ta daina kira ta dauki
alwashin idan ta dawo zata gane kurenta, shiru nazia har qarfe goma bata
dawoba, sai hankalin inna ya fara tashi, ta dauki waya kena zata kira yaya
hafeez sai gashi yazo, kasan fa har yanzu nazia bata dawo ba!??, haba dai,?
Allah kuwa! Kuma nayita kiranta bansametaba, to baki kira qawar tataba? Eh ban
kiraba, to bari in kirata.
Saida ya kira sau uku ana
hudu aka daga, batayi maganaba shi ya fara sallama aka amsa mishi sama sama,
yanxu inna take gayam nazia har yanzu bata dawoba! Kuma tace gidan ku xataje
kamar yanda kika roqa na amince ta tafi, tace Nazia kuma?? Ai batazo nan ba!!
What?Eh batazo ba nace, ai kuwa tun safee tafito gida tace zatazo gidanku,
kamar yanda kika buqata inna ta barta tazo, hmmm to kuwa banan tazoba, sai ku
kira wayarta kuji ina yarku take.! Ban..... yaji ta katse waya bata ma saurari
abinda zai ce mataba, ya juyo yayiwa inna bayanin abinda khadijar ta fada
hankalinsu duk ya tashi, suka fito aka fara chigiya unguwa unguwa har kofar
rini unguwar su sista khadee saida akaje nemanta, amma bata ba labarinta, gashi
dare yayi, haka suka kwana zaune, ga wayarta na ringing amma ba'adauka guraren
asuba ma wayar saita daina ringing hankali ya qara tashi, tunda asuba yaya ya
koma police station aka kai hotonta ana cigiyarta, aka kai gidan tv gidan radio
jarida duk aka baza ana nemanta, amma har guraren 12 na rana ba ko karenda yace
ya ganta,
Tana zaune ta tanqware
gafafu, taji ana murda qofa, tuni ta miqe tsaye tana jiran shigowarsa, yana
kunno kai dakin da sallamarsa da murmushin sister har kin..... sai saukar mari
yaji a fuskarshi, kai mahaukacin inane da xaku kawo gidan maxa ku ijiye, idan
ita khadijar yar iska ce to ni ba yar iska bace kuma ka gaggauta maidani gidn
mu...!!! ya dago da sauri ya kalleta, ya daga hannu zai mareta kome ya tuna
kawai ya sauke hannunsa,ya dunqule hannu rai bace ya mata wani kallo ya wurga
ledar da ya shigo da ita ya ja qofa ya kulle ya tafi abinshi, sai tafara dana
sanin hukuncin da ta mishi, tafara Allah wadai da zuciyarta,da kuma rashin
kunya irin tata, miyasa ta mishi haka?? Lallai bata kyauta ba gashi ya tafi ya
barta,jiya ta mare shi yauma ta mare Shi, itako haka xata qare da dukan
maxa..!!!!?
qeqe idonta ba kuka ba
alamunsu ta miqe ta janyo ledar Abincine take away guda biyu komai dai guda
biyu, da alama da nashi da nata dasu drink da ice cream duk a ciki, ta bude ta
sa abincin gaba amma ta kasa chi tayi tagumi ta tashi tayi sallah azzahar
tananan zaune har la'asar tayi sallah taga cikinta ya fara ihu, ta janyo
abincin taci ta qoshi,a haka bacci yayi awon gaba da ita har dare yayi bashi ba
labarinsa guraren sha biyu ta dauko abincin dazu, dayan da ya rage ta chinye,
shiru shiru har bacci ya dauketa bata farka ba sai guraren biyar, bashi ba
labarinsa, amma kuma ya ijiye mata ledar BF.
hakadai wasa wasa har saida
Nazia tayi kwana hudu a gidannan bata qara ganin saba, kuma kamar aljani sai
tayi bacci yake kawo mata abinci abin yana daure mata kai, yau ta dauki
alwashin bata ba barci, har kusan maqreeb ba'a kawo mata abinci ba, data gaji
da jira sai ta dan gyangyada baccin da tashinta duka minti hudune amma har ya
kawo abinci ya fice abnshi, tunani kala kala takeyi, ta fara tunanin ko ta
daina cin abinci ne, wata xuciyar tace ki danne abinki ko kin mutu kije da
nauyi..
Duk tayi wani iri da ita
ammafa bata rameba ko kadan dan kuwa bata wasa da abinci saidai akwai alamar
tashin hankali tare da ita,
Iyaye anyi sanarwa har an
gaji bata ba labarinta, anje gun malamai suna ta addu'a anata sauke qur'anai
Allah ya bayyanata amma shiru.. sister khadee kuwa bata ma san cewa har yanzu
ba'aga nazia ba, hankalinta kwance tana al amarrunta, ko a skull da andauko
zancenta sai tabar gurin batason zancen, bata San xancen batanta akeyiba, su
kuma sauran sun dauka haushin rashin qawane yakesa bata zama cikin mutane
musamman da ake cewa garin zuwa gidansu ta bata..
Yaudai baxanyi bacci ba sai
naga aljanin da ke ijiyemin abinci,baccin qarya nayi ya dauka nayi bacci ko
minti uku ba'ayiba naji ana buda qofa a hankali bayan ya bude sai kuma ya tsaya
kamar bayan minti daya sai aka turo qofa ina jin ya turo qofa nayi zubur na
miqe dama akan dadduma nayi baccin gefen qofane yana Shigowa na miqe dan Allah
uncle kayi haquri.!!! da abinda na maka dan Allah ka kaini gida, aranshi yace
dama batayi bacci ba??.
Ya tsaya bakin qofa ya
toge, ina tsoron in shigo ki mareni! Ko ki dakeni dan nakula bakida lafiya!!
Naji xafin maganar amma na Shanye yaci gaba idan haukar taki baxata motsaba in
shigo, kuuuuut dan na mareShi xaicemin mahau kaciya, na daqo na kalle shi namai
kallon raini har na hada baqar maganar da xan yaba mai, kawai na sunkuyar dakai
kayi haquri uncle.....
Yashigo dakin ya zauna, ya
kalleta ashe ganin da yake mata a camera ba haka bane duk ta firgice a camera
kuwa yana ganinta kaman lafiya lau,
Yana xama ta fara jero mai
tambaya...
Miyasa ka ijiye ni anan??
Mi kakeso in maka??
Baka tsoron Allah ne??
Ko kai ba musulmi bane??
Baka tunanin halinda
iyayena zasu shiga??
Is ok.... ya katseta, da
daga mata hannu kansa na kallon qefe, ta dago ta kalleshi, ki natsu kiji mi zan
gayamiki!! Na farko Idan na fara magana kada kiyi magana sai na qare, kinajina?
Eh naji!! Ya juyo ya kalleta tausayinta da yanda ta bashi amsa ya kamashi ,
lokaci daya sonta da sha'awar kusantarta ya kamashi, ya hade yawun dole, gashi
ta wani mishikyau, tufafin sa ne a jikinta top da wando, yayi sauri ya kawar da
kai, ya miqe tsaye idan har ya kuSan ceta bai mata adalciba, dan kuwa yayi
niyar keta mata mutunci ladar mari da ta mishi amma kuma tausayinta ya rinjaye
shi, ya miqe anjima zan miki bayani, zatayi magana, mi nace miki?? Ta tuna yace
kada tayi magana, ta kalleshi taga idonsa taga ya kada yayi jaa, sai taji
tsoro, ya fita, mamaki ya kamata yanda ya sauya lokaci daya, taci abincin tayi
sallar tana nan zaune sai gashi ya shigo, abin mamaki bai kalli ko gefenta ya
zaune ya juya mata baya.....
WALIYYI kenan..
Ya allah kabamu xuciya bamesan sa 6amakaba..