BawaddaTakaini kyau bare
suce ni mummunace, Lokaci daya naji na tsanesu dukan su na tsani rayuwar birni
ma, ina tsoron in musu magana akan dariyar da suke min in gudun su faramin
turancin iskanci dan na kula ba wanda yake Hausa cikin su, haka na kama
mutuncina, na zauna a clss din a quntace ba dadin rai har aka tashi break fast,
sai yanzu na tuna yaya bai bani ko gwandalaba, Kuma gashi banzo da wayataba,
haka dai na zauna idona sukayi rau rau, kamar zanyi kuka, ina zaune ni kadai
wata yarinya tashigo ga dukkan alamu na girmeta, sister bissimillah ko, nidan
bansan miye takeshaba dan yaya baitaba kawo mana irin abin ba, nayi murmushin dole,
no na gode, tayi dariya ai wallahi saikinci, ta bani dariya yanayin rigimarta
kamar fatimata ta qauye,kuma ga kama da sukayi da fatimar nace aah ina azumine
da yake yau Monday da mizai hana in siyo nima inci, ta kwashe da dariya,
nadauka ta gane qaryar dana sharamatane, ta kalleni kice dai qawar tawa
malamace, araina nace yaushe na zama qawarki haduwar minti biyu, ta kalleni
sunana khadija, Muhammad, ana kirana da sista kd, amma fili na maimata sunanta
sista kd, tace of course, ko sunan ba dadine, nayi murmushi araina nace kada ta
faramin turancin banxa,Aah da dadi mana inason in zabi wanda zan kiraki
dashine, tayi murmushi da yake ta cika baki da cake, ke ya sunanki, sunana
nazia Muhammad, itama ta mimaita sunan, yadai, no kamar na tabajin sunan ne a wani
guri amma na manta, nikuma araina nace nikam a gurin fatima ce naji sunan ki
sista kd , nice to meat you, nace thanks, na kasa daurewa nace nihal dan Allah
miyasa tunda naxo sukemin dariyane? Itama tayi dariya tace
Sabida kin saka sababbin
kaya baki musu iron ba, kinsan fa yanzu an waye an ci gaba, ba yanda za'ayi ka
saka sababbin kaya baka musu iron ba, ana ganinka za'agane kuma sai a maka
dariya, shi isa kikaga suna dariya, amma kada ki damu gobe idan zakizo sai koyi
qoqari kiyi iron din uniform dinki kamin kizo, araina nace da yake su yan birni
yan iskane ba dole suma mara iron dariya, a fili nayi murmushi, na kalli kayana
na tabbatar da cewa da gani an san sababbine, sai na fuske, na basar da
maganar, munanan har yara suka dawo break, malami ya shigo aka gaidashi anan
yake tambayata ni baquwace nace eh, sauran yan clss sai dariya sukemin, araina
nace wato rainin wayon hadda malamai akeyinsa, tun lokacin nayi marking din S/S
master, hadda shi a yiwa students rainin wayo, haka dai har aka tashi makaranta
zuciya ta cike da qunci da tsanar birni da mutanen birni, bayan an tashima
saida naga tasku, sabida kowa anzo an daukeshi, wasu kuma skull bus take kaisu,
ni kuwa bansan ko inaba bare inje kuma bansan kowaba, haka na zauna jikin gate
har 3:30 sannan yaya yazo ya daukeni, sister ya karatun dai? Ya naga fuskarki
ba annuri ko skull din bata miki ba,?? Na turo baki wallahi yaya ba skull din
bace students dinne basuda kirki, hakafa duk inda na wuce sunamin dariya, wai
banyi iron ba shima ya kalleni ya kwashe da dariya, au hadda kai yaya!?? to ke
sister ai dole a miki dariya kin saka kaya haka
Kamar wata kairat ahmad ba tsari ba komai, ban san lokacin da na qyalqyale da
dariyaba, wallahi yaya ka raina kairat ahmad dinnan, kuma ita ganin kanta
takeyi wayayyiya tunda ta zauna qasar waje,har ma yanda takejin da yaruka kala
kala.... ki barta shirmen banza takeyi, ni haushima takeba yanxu fa wani
abokina takeso dan zaria. Na qyalqyale da dariya, wallahi yaya duk sai na
gayawa gwagwo sharrin da kake yiwa yarta, ya harareni, kefa matsalar ki kenan
yanzu sai kije ki fada,? Sosai kuwa sai in fada mata kana tsinar mata ya, to ai
abokiyar wasan muce, gwago ba abinda zatayi, heheheee, Kullum da haka kake
fakewa kana zagar mata ya.
Da
hirar kairat "presenceszee" muka iso gida, ina abincina yunwa nakeji,
yaya yayi salati, sorry sister Wallahi sam na manta ban baki kudin break ba, mi
kikaci,? Nayi murmushi.! Banci komai ba hasali ma da wata sis kadee ta min tayi
cewa nayi azumi nakeyi, Yaya ya zagayo ya dafa kaina, kiyi haquri sister Allah
namanta sam.! Laa yaya ba komai fa, ai nasan mantawa kayi idan ba mantuwa ba ba
yanda zaka barni da yunwa, yauwa kici abinci ki huta anjima zamu je day to day
shopping, idan kin kammala ki kirani...