AsheShekara14 A duniya, tun ina cewa a kaini birni gurin mijina har na daina da na fara wayo na fahimci ba sona yake ba, lamarin qauye ne kawai, gashi kuwa mahaifina yace bai yarda in auri wani idan bashiba, kuma kowa ya san ni matar nura ce, amma nura sam bai damu da harkataba, bai damu daniba, ko.qauye yaje gurin mamarshi baya kwana ranar da yaje ranar yake dawowa ban taba qaninsaba sai dai yakan yomin tsaraba tuli tuli, nida fatima, da alama ma iyayen fatimar ne suke min siyayyar, sabida komai iri dayane nida ita, shi isa shima yayana komai iri daya yake mana da ita, Allah sarki fatima ko Yaushe xamu qara haduwa gashi tace xata bani address din qanwar ta idan naxo birni muyi qawance amma naxo tna skull ina cikin wannan tunanin sai naji kiran inna natashi naje, kizo ki hada mana abinci idan kin iya nidai kam ban iya aiki da gas cooker ba, nace nima ban iyaba, nadauki a shana naje gurin da ake wancan ginin na tattaro itace na hura wuta na mana girki, muka danne abinmu,har lokacin fuskar inna a daure take narasa yanda xanyi in bata haquri sai bayan magreeb yaya ya dawo yashigo da ledodi,dayar ledar tablet ce da kuma wayoyo guda biyu, ya bani tab din ya hadamin da wayar, da sim itama inna ya bata wayar ya nuna min yanda ake kunnawa da kashewa da Sauran abubuwan duk dai fuskar shi ba yabo ba fallasa amma yaqi bari mu hada ido yace zancen skull dinki gobe zan kaiki makarantar da zakiyi karatu sai kiganta dama anyi komai kaiki kawai xa'ayi, naji dadi Sosai a raina da jin zancen makaranta sabida har nakai jss3 nayi jlc kawai aka shigo da zancen birni, yaya ya juyo gun inna ya sassauta murya, ya fara baiwa inna haquri abinda ya faru dazu da safe, inna tace ba komai nima nan na Sami dama na bashi haqurin rashin ta idon da na masa, dan uwa rabin jiki aka yafi juna muka dawo kamar yanda muke ada, farin cikina ya qaru ganin cewa yaya na da innata sun daina fushi dani, duk mun saki jiki kamar ba'abinda ya faru da safe har na bama da yaya labarin yanda mukayi girki, yasha dariya, qarshe yace za'asamo wa inna wacce zata tayata zama da aikace aikace tunda ni makaran zan riqa zuwa, dagyar dai inna ta amince da mai tayata zama, mun shiga kitchen yaya ya nuna min yanda ake amfani da komai, mukaje bayi yanuna min yanda ake komai da komai, munyi hira Sosai dashi daga bisani ya wuce dakinsa nima nabi inna dakinta dan nasan bazan iya kwana ni kadaiba, naje muka fara hira nida inna ta, acikin hirarta dai ta hada da wa'azi, ta qara jan hankalina akan zafin rai irin nawa, taja kunnena akan yanzu nashigo wata sabuwar rayuwa mutane daban komai daban so dole sai na san yanda zan riqa hulda da mutane, kuma ta ja min kunne daga yin mugayen qawaye, da kama kai kada in riqa shishigi ga wayanda suka fi qarfina, in kama mutuncina insan cewa ni ba kowa bace, ta qare muka dauko waya na nuna mata iya abinda na gane nasan kuma zata gane, ni kuma nahau daddana tawa ina qara fahimtar abubuwa, haka dai har bacci mai nauyi ya daukeni nabar inna tana ta kallon wayarta,dama tunda asuba yaya yace in shirya zai wuce aiki yanason ya kaini skull,din mu ai ko dan kada amaimata dan gidan jiya tun asuba ban koma bacci ba, bayan mun qare break fast muka dauki hanyan makarantar da za'akaini, tun daga nesa na hango hadaddun motoci suna sauke yaransu, nasan cewa wannan skull din ta well to do ce, araina nace yaya ya kawoni gurin yayan masu kudi, tun bamu isa admn block ba na ba na fahimci wasu yara yan mata suna ta kallona suna dariya, araina nace ko dai sun gane cewa daga qauye nake, haka na fuske abina,sabida nasan banida munin da za'amin dariya, haka ni bana tafiya bazar bazar " kamar 6* mrdy" bare ince na kwafsa, to dai haka har muka iso admn block ina tunane tunane, matsalar farko dana fuskanta rashin iya speak da English , ina gane duk abinda ake fada amma bana iya bada amsa, shima dai da ni daqiqiyace da dan karatun qauye ba abinda xan iya yaya ya bada C. A dina daya karbo a qauyenmu, akamin interview dagyar dai suka aminta na zauna jss3 maimakon ss1 da zanje, shima jss3 din s aida yaya ya dage dan jss1 sukaso su kaini tunda bana iya magana da English, admn off ya kira wata yarinya yace ta nunamin clss dinmu, ta kuwa nunamin nashiga nayi sallama da yaya, na wuce clss Lallai sabuwar rayuwa da mutane kala kala, abinda yafi bani haushi kallona da suke suna dariya na qare musu kallo kaf ba wacce takaini ko kyau bare ........
click here
Ashe Kaine Mijina Part 1
Ashe Kaine Mijina Part 2
Ashe Kaine Mijina Part 3