Amma ya zanyi fuskewa kawai
zan cigaba dayi yaya yashiga mota nima nashiga, nasani sarai idan akwai abinda
ya tsana baifi ashiga bayan mota a barshi shi kadai a gaba ba, na kuwa fuske
nabi Inna baya, ya kalleni irin kallon tausayi muka hada ido amma na fuske
abina, na bude baya zan zauna, Inna tace nan kika saba zama?? Sumui sumui naje
gaba na zauna, yaja mota sai sakwato birnin shehu, sokoto garin dan fodiyyo
garin karamci qarin mutumci, garin dattako, garin kashe kunya, na jinjina muku
sakwatawa, Allah ya barmu da qaunar ma'aiki.!!
Tunda muka shigo nake raba ido sabida qarin yamin, Gaskiya qarin
yanada kyau da tsabta, sai kalle kalle nake sabida tunda nake ban taba zuwa
sokoto ba sai yau, rabona da sokoto tun ina shan nonon innata, haka kawai naji
hawaye suna saukomin, Lallai ban kyautawa yayaba! Na mishi butulci Sosai, shine
wanda Kullum burinsa ganin farin cikina! Shine Kullum burinsa farantawa
mahaifiyata,! Muna qauye amma ba wanda zai kirani da ba qauya! Ba wanda zai
rainani, a qauyen mu nice gwana, nice yar gayu, nice kowa yakeso, kuma duk
albarkacin yayanane, yanzu haka da na shigo cikin birni duk yan matan da na
riqa hangowa a mota, ba ko wacce na gani da irin tufafinaba, sai daidaiku, cox
yaya yayi ta fadamin tufafin da yake min ai na manyan matane dinkin ma haka,
tufafina masu tsada na yayan masu kudi amma shine zan yiwa butulci irin wannan
gaskiya dole in bashi haquri, na dan faki ido na kalleshi, sai ya qara bani
tausayi,matuqa narasa irin halina, tun bayan rasuwar mahaifin mu munsha wahalar
duniya, wanda daga baya yaya yana karatu yana bin motar daukar kayan gwari
irinsu ayaba da lemo da mangoro, duk dai wani fruits da ake yayi, haka zasu
loda cikin mota idan sun isa gari sai su sauke, ana biyansu, kuma ahakan yake
karatu yana wannan sana'ar har ya qare secondary anan mai gari ya dauki
nauyinsa da yake mai qarin mu abokin marigayi babane, ya dauki nauyinsa yaje
dan fodiyyo sokt anan yayi dgr na farko yana kammalawa ya fara karantar wa a
sokoto cement primary anan dai ya sami kudin shiga Sosai har ya ci gaba da
karatunsa, duk albashinsa akan mu yake qarewa sabida yaya mutum ne mai zuciyan
yi kuma yanada son fitarda kanshi dama wani nashi kunya shi isa tun yana qarami
da yake dako kayan kwalliya ina dasu komai yana siyamin har na tasa nadan
girma, kuma sam bashida qyashi duk abinda ya samu inna da naxia,
Mu biyu muke a gurin mahaifin mu ni da yaya, mahaifin mu
ma'aikacin prison ne yana gadi a sokoto prison a wani rikici da akayi a gidan
yari aka harbeshi anan Allah ya karbi ranshi, tun daganan muka dawo qauyen
mahaifiyata da zama tun ina shan nono ataqaice dai bansan mahaifinaba. sai yaya
da inna tsakanina da yaya shekara takwas ne, sabida inna tace har ta daina
tunanin haihuwa sai ta sami cikina ta haifeni, yaya na matuqar sona kamar shine
babana, bansan wahalar rayuwaba sam,
Ki fito mun iso naji ya fada cikin sassanyar murya, tausayinsa
ya qara kamani, ban san lokacin da na masa murmushiba, amma sam fuskar sa bata
kaina, gidan da na gani ya tsoratani, wani fakacecen gidane, da gate yaya ya
bude, muka shiga, naga ikon Allah araina nace a cikin wannan gidan zamu zauna,
sabida ko a mafarki ban taba ganina a iran wannan gidan ba, gidane bangare biyu
ban gare daya an kammala ginin dayan banqaren kuma ba'a kammalaba amma wanchan
bangaren da ba'a kammalaba yafi banqaren mu girma, muka shiga, muna shiga na
tabbatar da yaya yamin gatan da yake fadar zai mini, naga so da qaunar da yace
zai nuna mini, tabbas nayi sa'ar dan uwa, wasu hawaye suka sake zubomin, yaya
ya shigo da kayan mu, ya nuna min dakina komai a tsare hatta kayan make up an
saka min toilet dina sai wanda ya gani dakin inna ma haka komai tsab an gyara,
sai dayan dakin da ya nuna mana na baqi, ya nuna ma inna kitchen da kayan
abinci da komai a ciki duk da tana daure masa fuska yana mata bayanin komai
nima yamin bayanin komai amma yaqi bari mu hada ido yayi waya yace aturo yaron
sun iso, almajiri ya nema mana wanda zai riqa mana cefane da sauransu, ya baiwa
inna kudi kamar yanda ya saba sai kawai yace sai anjima ya fita, nida inna
mukayi jugum jugum sabon gida sabuwar rayuwa, Lallai yaya ya cika min
alqawarina, sabida ya kawo ni birni kamar yanda kullum nake cewa inason akawoni
birni gurin mijina, yau gani a birni a birnin ma sokoto birnin shehu, gari mai
kyau kuma gida mai kyau, in kalli inna ina tsoron in mata magana naga ta daure
fuska, sai na tashi nashige dakina, nayita kalle kalle, komai a tsare kuma tsab
dai dai da buqatar duk wani dan birni, hotona dana yaya da inna munyi kyau
Sosai anyi babban frame dinsa an kafa a dakina, nayi kyau a hoton yarinta na a
fuska qarara amma bai hana kyauna fitowa ba, yar qaramar fuskata das da manyan
idanuwana das dasu, hmmm gaskiya nayi kyau a hoton, na zauna jigum, sai na fara
tunanin qawayena na qauye fatima yarin yayar nura ce duk qauyen mu ita kadai
tamu tazo da ita sabida itama yar gayuce iyayenta suna birni amma ita tana
qauye abinta, nura shine wanda tun da mahaifiyata ta sami cikina yace idan mace
aka haifa matarshice, hak kuwa akayi tunda aka haifeni ya ke sona ana cemin
matar nura, mamanshi takance dani auta matar auta, tun inada shekara uku, ya
koma birni gurin yayanshi baban fatima qawata ban qara ganinsa ba har yanzu da
nakeda shekera 14 a duniya...yanxune labari zekankama..!