Ke nazia kiyi sauri ki tattaro kayanki kizo mu tafi yayanki yana jiranmu, ko wallahi mu tafi mu barki! ganinan zuwa inna! nazia ta baiwa inna amsa tana qoqarin fitowa daga dakinta da dan gunshin kayanta a hannu, da yar jakarta inna ta kalleta a hantare, kekam kinji haushi Kullum idan za'afita sai an barki, duk zumudin da kike ya zama na banza tunda har na rigaki shiryawa, nazia ta kwashe da dariya, wallahi inna kinsan kayana sunada yawa shi yasa ban samu na fito da wuriba, ke dan Allah wuce ki bani guri ko in hantareki, mara kunya, dama haka kike kullum da baqar shiririta, ta qara kwashewa da daria, hadda gyagyataWa, duk wanda yaga nazia a gida idan ya ganta a waje zai dauka ba ita bace, yanda take daure fuska kamar bata taba murmushi ba,(kaman aysha humaira kenan) zaka dauka kamar ma bata taba dariyaba a rayuwarta,tafito da dan gudu gudu tana kallon ko ina idan basuyi Mantua ba ta kalle ko ina amma komai babu tafito tana murmushi, yayanta ya kalleta, ke wallahi kinci albarkacin inna da sai mu tafi mu barki kinfi kowa cewa a koma birni amma kuma kinfi kowa shiririta,
mtsww yayi tsaki, ta qyalqyale da dariya abina na fada jikinsa yi haquri yayana, yanzu ai gashinan na fito mu tafi ko, amma fa abu daya ya rage min, inna da yaya duk suka juyo suna kallon juna da mamaki, inna tace dama baki kammala ba Nazia??? aah inna na qare komai .
Amma ai kince inje gidan su abban fatin birni in musu ban kwana,
Inna ta saka salati tana tafa hannu, dama nazia da nace kije ki musu sallama bakije kin musu sallama ba, yar duniyar ta qara kyalkyalewa da dariya, amma anyi shaqiyiyar yarinya inji inna, ta kawo min duka amma ina na kauce, na qara kyalkyalewa da dariya, mutuniya banza, sai ta ishimutane da dariya sai kace mai tabin jinnu, yaya ya gama qufula, baice komai ba.!!! Na zabga a guje ina ta dariya, ina shiga dayar kwanar na daure fuska, kamar banice mai kyalkyala dariyannan ba, na gyara hijabina nashiga gidansu hafizun birni mamanshi tana ganina ta hau washe baki,tana min kirarin da ta saba amma ko ajikana nasha magani abina tace auta matar auta, badai tafiyar ceta tashiba, kamar banason magana na kebe baki nace, E, tace yar nan Allah ya kaiku ya lafiya gashi sameer baya nan da sai in ce ya baki number yayan naki nura idan kunje sai ku nemishi ku riqa qaisawa, bance mata komai ba, ta qare surutanta, nace zamu wuce su yaya hafizu suna jirana, tace to yar nan Allah ya miki albarka, ta bani kudi wai insha ruwa a hanya amma naqi in karba, nace ina fati take? Allah sarki bata dawo makaranta ba idan ta dawo xan fada mata kun tafi, xatayi kewa Wallahi xan wuce yarnan baxaki karbi kudin ba nagode hajiya, dama itama ta sanni da taurin kai aranta take cewa tauri da tauri
Sai qaqa, koda na qaraso na tarar da an kulle gidan mu kuma ba motar yaya ba labarinta!!! Tuni hanjin cikina suka shiga kadawa idona suka cika fall da hawaye sai kuka, yanzu su yaya da inna sun tafi birni, kuka Sosai nakeyi na zauna dirshan a qofar gidan mu na rufe ido ina kuka,maimakon in dan xagaya amma anan na dabe ina kuka, sai ji nayi ankwasheni da mari ta gefen fuskata ! Kutumar uba waye yake dukana duk da ina cikin qunci amma da bala'e na dago kai inga wane dan iska ne yake dukana!!! Daga kan da zanyi sai kawai naga yaya, fuskar nan a turnuqe kamar an aiko mishi mutuwa, wallahi idan baki tashi mun wuce ba zan babbalaki anan, mamaki da tsoro ya cikani, araina nace su tafi su barni sannan kuma yaxo yana dukana da zagi, araina na fara balaee na daure fuska, ashe nice banida kai mota gatachan gaban gidan mu kadan kwana sukayi suna jirana, da yake ni idan ina tafiya bana qage sai ban hango motar ba, na kuwa sha kunu na fuske abina, ya shiga gaba ina bin bayanshi saida muka isa jikin mota naja na tsaya, kamin kace kwabo inna ta wankeni da wani marin,ta buda baki xatayi magana na rigata nashiga uku, nace minayi muku kukeson ku kasheni,sai inna ta shige mota ta barni, naci gaba dan kunga ina zumudin zuwa birnin ne ake min wulaqanci...!! to Wallahi na fasa zuwa birnin banaso, bazanjeba a saukemin kayana...!! ba inda zanje, na qara fashewa da wani kuka....
yaya ko kallona baiyiba shima ya zagaya ya shiga mota ya kunna yana jiran in shiga amma ina taurin kai ya motsa, ko ajikina, yayi horn alamar in shiga amma ina sai ya fito ......,
KUNASOO??????
KATSALANDAN YAYI qaura insha allahu nan gaba kadan xamucigaba sabida wasu dalilalai..
Shayasa xan baku wannan ku haquri dashi..
Title :
Ashe Kaine Mijina Part 1
Description : Ke nazia kiyi sauri ki tattaro kayanki kizo mu tafi yayanki yana jiranmu, ko wallahi mu tafi mu barki! ganinan zuwa inna! nazia ta baiwa inn...
Rating :
5