Ina take rabi!!!???
Gatachan dakina, mi takeyi
a dakin ki kuma da gudu ta qarasa, tana ganina ta rungumeni, duk da warin
kwatar bai saki gashinaba, amma haka ta rungumeni tana kuka,kin bani wahala
naziah, ta janyo hannuna muka shiga daga cikin gidansu, dagyar nake tafiya, ga
sanyin da nakeji, mun shiga gidan kenan, bamu kai parlour ba naji murya daga
baya ke ina kika samo wannan almajirar??
Sis khade dai kam ko
waigowa batayiba bare ta bashi amsa,! Yaci gaba da magane, ke badake nakeba,
wallahi idan nazo gurinnan sai na babballaki, haba uncle ba girmankabane wannan
abin da kakeyi, da talaka da mai kudi duk Allah yayisu,kuma ai wannan naziah
dina ce fa.!! Kece naxoon taki almajirace amma kuma akwai diri, dayake duk
kayan sun manne min a jiki shape dina ya fito, najuyo na kallashe, fitsarar ta
motsa na kalleshi daga sama har qasa na zubar, na hada da tsaki, sis khadee ta
kalleni, haba nazia, qanin abbanmunefa, na fuske ko qanin abbankune ai baisan
darajar mutaneba, koma miye ai uncle dinane, kamin ta rufe baki tuni naji
saukar mari a fuskarta kamin in ga waye nima ya kwasheni da nawa marin guda
biyu lafiyayyu, saida na gigice,Ciwon kai ya qaru na bude ido naganshi gabana
tsaye, kuuuut idan na barshi Lallai ya daki banxa, nima nasa hannu na kwasheshi
da irin nashi marin guda biyu lafiyayyu....
Mamaki ya kama sista khade, taga yanda na mari ganin mahaifinta, wanda yake ji
da ita, kuma a gabanta a gidansu.!! Lallai koda uncle ne bashida gaskiya dole
ta nuna ma naziah kuskurenta dan gaba...!!
Sista khade ta kalli nazia
tace, ke dama yar akuyace??? Wacce batasan darajar na gaba da itaba?? Wallahi
da nasan ke butuluce da bazan taba qawance da yar qauye irinkiba.!!
Mamakin duniya ya cika
nazia dama haka sista khade take mara mutunci to ba qyaleta zanyiba, wata
zuciyar tace ki gyaleta gidansu kikaxo, sista khadee sai masifa takeyi, inda
take shiga ba nan take fitaba, zuciya ta rufe naziah uncle yayi Sokoko yana
saqa Wulaqancin da xai mata, ni kuma ga mugun jirin da ya qara tasomin ga sanyi
inaji ga yunwa, na dunqule hannu nakaiwa sista khadee wani wawan nushi, kuma na
kamata da duka baki, sai jini, unle yana tsaye riqe da kumatu yana dada kallon
wai almajirace zata mishi wannan wulaqanci yana chi gaba da saqa sharrin da zai
mata kuma yasa a ma danginta wulaqanci, sai ganin yayi ana kokowa, tuni ya
hanbare ni a wurgar dani gefe, ina miqewa na kama hanyar dana ga na biyo mun
shigo na samu na fita gidan nakama hanyar titi kamar mahaukaciya, ga warin
kwata gashi ina layi kamar yar maye, gashi banida ko kwandala na shiga taxi,
ina tsaye idona sun fara rufewa naji qarar mota gabana, sai jin nayi yace ina zuwa
na fada mishi unguwarmu tuni
ya bude min nashiga, ina shiga motar ban qara sanin inda nakeba
topah ga aikinnan..yau akeyinta..
Ñext episod..