in kin Kammala ki kirani a waya sai muje ko, Ina qoqarin dura lomar a bakina nace mishi to yaya, ya wuce, naci gaba da chin abincina ina baiwa innata labarin rashin kirkin yan makarantamu, da kuma qawar da nayi sis khadee, da kuma tsinar da yaya ya riqa yiwa kairat ahmad a mota, inna itama dariya tamun, ai sai na hada yayanki aure da kairat ahmad muga qarshe tsiya, na kyalkyale da dariya, wallahi kema kinsan inna zakisa kawai ya qara tsanartane, dama haushinta yakeji, Allah sarki kairat nifa bana ganin abinda yaya yake cewa tana dashi, kawai tanada dan Rawan kaine, inna tace nidai ba ruwana,nayi murmushi, muna chin abinci muna hira har na kammala, inna bari inje in danyi bacci, inna ki tayar dani 4:30 pls, to Allah yakaimu,
Kamin biyar dagani har yaya mun gama shiryawa, har munshiga mota muka dauki hanya sai DAY TO DAY, gurin ya hadu Sosai, super market ne hade da restaurant da kuma park a gurin, nidai kam fuskewa nayi kada a gane sabon shigace ni,amma Lallai gurin ya burgeni matuqa na sha magani ga shigar da nayi nasan qaryar yan birni Su nunan dressing, ina tsotsan minti na a hankali, irin nima yar birnin nan dan na kula birni yan rainin wayone Sai Su nemi Su min dariya wannan karon kuwa na shirya chin uban Su,Munshiga day to day, munyi shopping, kayan make up, ba qara kwasowa da turaruka kala kala da Su chocolate ba abinda bai siyamin ba, muna fitowa cikin ikon Allah na hadu da Sis khadee sunzo siyayyah,itada wani hand some guy, araina nace kar dai Saurayinta ne, dan yanayin yanda naga yana bata kulawa ko motsi tayi a kan idon sa sai kuma Suka burgeni, naziah wannan shine ammar shi xan aura Insha Allah, ta wani lumshe ido ta kalle shi, shi ko wawan Sai murmushi yake, tace wannan fa ko dai shine angon namu,tuni yaya ya daure fuska, na kalli yaya naga yasha magani no yayane fa....!! Ta dan sosa kai irin taji kunyar nan, ta gaida yaya na gaya ma yaya itace wacce ta min mutunci suka gaisa da yaya, yadan saki rai, mu dan kebe da ita ke mutuniyar ai na dauka wannan kamu kikayi guy haka har guy, uhummm kina tare da ammar dinki kina kallon wani, tayi dariya aike ba'a tsayawa guri daya ne, har na fara joules naga saurayinki xaifi my ammar, mita gani kuma tace kai ammar dina fa qarkene araina nace wannan yarinya da saurin sabo take, muka danyi tadi muka sha ice cream tare daga baya mukayi sallama muka wuce, muka dawo gida cike da farinciki.....
Kwanaki sun shude, watanni sun haura shekaru sun jaa qaba, nida sis khadee mun zama daya, mun zama qawayen juna, fiye da tunanin mutum dan kuwa komin ta yayi kama dana fatima na, mun zama abinda muka zama a skull,amma nafita wayo, duk wani neman magana ni nake turata tanayi amma ita bata ganewa kuma bata ganeba, idan akazo in fuske a mata bulalarta, koda tace ni na turata ba wanda yake yarda sabida kowa yana min kallon waliyiya dan ba mai ganin koda murmushi na bayan ita...
Duk wannan shaquwar tamu da nihal kusan shekara biyu amma tunda nake sau daya na taba zuwa gidansu, sabida yaya baya bari, hattana qawaye baya bari inayi barkatai, bare zancen samari,
Nihal ta roqi yaya da kanta, akan ya barni inje gidansu, haka kuwa akayi yaya ya barni amma bazai kainiba sai dai in shiga motar kasuwa sabida yana da aiki sosai a office, ban damuba coz inason fita, na shirya tsab na musu tsaraba, na nemi motarda zata kaini unguwarsu, saida na fito na fuskanci garin akwai hadari sosai, na sami mota na shiga sai unguwarsu nihal, kofar rini...., ina isowa unguwar hadari ya fara tasowa tare da iska, duk wanda yasan hadarin Sokoto yasan yanda yake da iska mai hade da qasa a ciki, idona suka cika da qasa, har bana ganin gabana sosai, unguwar ba kowa, tayi shiru sai qarar itace da suke kadawa kakeji, kowa ya shige gidansa, iska akeyi sam bana ganin gabana, sai samun kaina nayi cikin qaton ramin kwata tsundum, Subahanallahi..... na fara swimming a kwata(dama andade ba'asaduba sukairat),mai uban wari ga kaina da ya bugu, haba ga ruwan sama an farayi kuma da qarfi, na tabbatar da idan ruwannan sukafi haka qarfi wucewa zasuyi dani, na tabbatarda kuma mutuwa ta tazo, dagyar Allah ya taimakeni na fito ramin nan, ruwa kamar da bakin gwarya, na fito amma na baro jakata jikin kwata, kuma gashi tace idan na iso in kirata, dan ban gane kwatancen da tamini ba gashi wayar na cikin jaka, jaka kuma na cikin kwata, sai qaqa....!!
ga ciwon kai buguwar da nayi, nasan ba taxin da zata daukeni haka dame dame da kwata in bata mishi mota, nasan ko na sami mota banida ko kwandala, haka naja jiki na rabe jikin gate din wani gida, ina tsaye sai ga wata mota tazo music ne yake tashi sosai, saida suka iso kusa dani suka tsaya suka kwashe da dariya, nadago na kallesu, bance komai ba ba bakin musu tsiya, sukayi horn aka bude musu suka shiga gidan, araina nace dole in bar nan gurin
Dan yaran gidannan da alama basuda kirki dagani yan iskane, na duba gabas da yamma ba mafaka sai nan, sai kawai na haqura har a qare ruwan kunyar duniya ta isheni, jikina duk kwata, ga ciwon kai ya tsananta har na kasa tsayuwa na tsuguna, ruwa yaqi zaqaitawa sai.....Yaqi tsaqaitawa Sai na yanke shawarar bari in daure in dan shiga ruwannan idan kwatar jikina ta wanke, my be zan samun abin hawa, na miqe kenan kawai sai jiri ya kwasheni na fadi a gurin sumammiya, kaina ya qara bugun gate din gidan,kikaji gwall, maigadi ya fito ya ganni a hakan ya shiga ya kira matar sa aka taimaka masa ya shigo dani daga ciki, shida matarshi suka taimakamin har na farfado na dawo hayyacina, amma bana gane komai kuma ban san inda nake ba, matar ta ciremin kayan kwata ta daurayemin jikina ta saka min wasu tsummakaronta,ta bani dan paracetamol da panadol na kora, bayan kamar awa biyu na fara farfadowa, na gane inda nake, suka tambayeni sunana da komai na musu bayani, muna cikin magana najiyo muryar sis da wani namiji a waje
Uncle wallahi tun kamin afara ruwa tacemin ta fito, gida, kuma batasan nan gidan ba, na kira wayanta yafi sau dubu baya shiga, kataimakeni dan allah uncle, kinsan Allah, wallahi ba inda zani gwanda ma ki haqura ki kama kanki ke idan ma kika qara min maganar wata anan sai na babbalaki....
Tabbas muryar nihal ce kuma ni take nema, nace ma matar maigadi, gurin waccan yarinyar nazo, tanajin haka tayi wuf ta tashi, ta qwala mata kira.. sis khadee.! Sis khade!! Ko ta waigo ta wuce abinta, sista khadi kizo ga nazia anan, ba shiri ta waigo ba shiri ina take rabi??.....
SABAHUL KHAIRR...!