A yau ne aka rantsar da dan Nijeriya, Dokta Akinwumi Adesina a matsayin sabon shugaban bankin raya kasashen Afrika watau AfDB.
Adesina ya maye gurbin dan kasar Rwanda, Donald Kaberuka wanda ya jagoranci bankin na tsawon shekaru 10 tun daga shekarar 2005.
A cikin watan Mayun da ya gabata aka zabi Adesina wanda shi ne tsohon ministan ayyukan gona a Nijeriya.
Sabon shugaban ya ce a cikin shekaru biyar masu zuwa, bankin zai mayar da hankali ne a kan samar da lantarki a gidaje da kuma gina asibitoci da kuma makarantu.
Adesina ya ce dole ne a mayar da hankali wajen samar da ayyuka a tsakanin matasa a Afrika saboda a cewarsa, matasa su ne babban jarin Afrika.
Title :
An Rantsar Da Adesina A Matsayin Sabon Shugaban Bankin AfDB
Description : A yau ne aka rantsar da dan Nijeriya, Dokta Akinwumi Adesina a matsayin sabon shugaban bankin raya kasashen Afrika watau AfDB. Adesina ya m...
Rating :
5