Hatsaniya ta barke a filin Idi da ke Ilori babban birnin jihar Kwara inda wasu mutane suka yi jifa a kan ayarin manyan mutane da suka je Sallar Idi, ciki har da shugaban majalisar dattijai, Sanata Abubakar Bukola Saraki.
Shaidu sun ce mutanen da suka yi jifa da ledojin ruwa da duwatsu, suna korafi ne saboda gazawar gwamnatin jihar Kwara wajen biyansu albashinsu kafin ranar Sallar.
Bayanai sun ce mutanen na ta ihun cewar a "biyasu albashinsu", kafin daga bisani jami'an tsaro su wuce da Sanata Bukola Saraki da gwamnan jihar, Abdulfatah Ahmed da sauran kusoshin gwamnati.
A jihohin Nigeria da dama ma'aikantan gwamnati ba a biya su albashi ba kafin ranar Sallah.
Title :
An jefi Bukola Saraki a filin Idi
Description : Hatsaniya ta barke a filin Idi da ke Ilori babban birnin jihar Kwara inda wasu mutane suka yi jifa a kan ayarin manyan mutane da suka je Sal...
Rating :
5