Dakarun tsaron Kamaru sun hallaka mayakan boko haram fiye da 17. Kamafanin dillancin labaran Reuteus ya habarta cewa a jiya Talata, Ma’aikatar tsaron kasar Kamaru ta sanar da wani farmaki da Sojin kasar suka kaiwa mayakan boko haram a yankin Amchide dake arewacin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar hallaka mayakan boko haram din fiye da 17. Ma’aikar ta ce da farko Sojin kasar sun samu labarin taruwan ‘yan ta’addar ne a yankin , lamarin da ya sanya suka kai musu wannan farmaki.
Daga farkon shekara ta 2014 zuwa yanzu kungiyar ta boko haram ta kashe fararen hula fiye da dari hudu a kasar Kamaru, har ila yau daga farkon billar kungiyar a shekara ta 2009, kungiyar ta hallaka fiye da Mutane dubu 13 a kasashen Najeriya, Nijer, Kamaru da Tchadi, sannan ta yi sanadiyar raba fararen hula fiye da million guda da rabi da mahalinsu.
Yanzu haka dai a kwai rundunar hakin gwiwa wacce ta gumshi jami’an tsaron 8700 da kasashen Najeriya, Nijer, Kamaru ,Tchadi da kuma Benin suka kafa domin yakar kungiyar ta Boko Haram.
Title :
An Hallaka Mayakan Ashabab Fiye Da 17 A Yankin Amchide
Description : Dakarun tsaron Kamaru sun hallaka mayakan boko haram fiye da 17. Kamafanin dillancin labaran Reuteus ya habarta cewa a jiya Talata, Ma’aikat...
Rating :
5