Masana kimiya a kasar Afrika ta kudu sun gano kasusuwan wata halitta mai kama da mutum, wadda ke binne 'yanuwanta da suka mutu.
Masanan sun gano daruruwan kasusuwan na kwarangwal guda 15 ne a wani kogo na boye mai wahalar shiga a kusa da birnin Johannesburg.
Babu wani kwarangwal ko kashi da aka gani na wata dabba ta daban a wurin, wanda hakan ya sa masana kimiya suke ganin cewa ba ruwa ba ne ya kai kasusuwan wurin.
Masanan sun zartar da cewa duk yadda aka yi wannan wuri kabari ne kawai.
Halittar mai 'yar karamar kwakwalwa da aka sa mata suna Homo naledi tana cikin rukunin dabobin da masana kimiya suke dangantawa dana yadda mutane suke a yau. Kalman naledi na nufin tauraro a harshen Sesotho
Halittar ta rayu ne a nahiyar Afrika a cikin shekaru miliyan uku da suka wuce.
Title :
An gano kasusuwan wata halitta mai kama da mutum.
Description : Masana kimiya a kasar Afrika ta kudu sun gano kasusuwan wata halitta mai kama da mutum, wadda ke binne 'yanuwanta da suka mutu. Masanan...
Rating :
5