Gwamnatin Saudiyya ta kaddamar da bincike kan Kamfanin gine-gine na BinLaden, da ake zargi da laifin fadowar wata kugiyar daukar kaya a kan Masallacin Harami da ke Makkah wanda ya yi ajalin Maniyatta sama da 100.
A cewar Sarkin Salman na kasar daga yanzu sun dakatar da bai wa kamfanin Bin Laden, wanda ke cikin manyan kamfanonin gine-gine na kasar kwangilar gini, har sai an kammala bincike a kan su.
Hatsarin na ranar Juma'a ya kasance babban Iftila’i da ya fada kan Maniyatta tun bayan shekarar 2006 da turmutsu-tsu ya kashe daruruwan Alhazai.
Wannan dai na zuwa ne 'yan makonni kafin gudanar da Arafa, a yayin da maniyyata daga kasashe daban-daban na duniya suka hallara a kasar domin sauke farali.
A cewar masu binciken Kamfanin na da Masanaiya kan ruftawar kugiyar da ta raunanta kusan mutane 400 ba ya ga wadanda suka mutu.
Yanzu dai an haramtawa Shugabanni Kamfanin ficewa daga kasar har sai an kammala bincike.
Kamfanini gine-gine Binladen Mamalakin Iyalan tsohon shugaban kungiyar Al-qaeda ne Marigayi Osama Bin Laden kuma sun kwashe sama da shekaru 4 suna aikin kwangilar fadada Masallacin na harami.
Title :
An dakatar da Kamfanin Binladen sakamakon hatsarin Makkah
Description : Gwamnatin Saudiyya ta kaddamar da bincike kan Kamfanin gine-gine na BinLaden, da ake zargi da laifin fadowar wata kugiyar daukar kaya a kan ...
Rating :
5