Hukumomin sojin Najeriya sun ceto wasu mutane 90 daga hannun kungiyar Boko Haram bayan da suka kori mayakan kungiyar daga kauyukan Dissa da Balazala na cikin karamar hukumar Gwoza ta cikin Jihar Borno.
A Najeriya hukumomin sojojin kasar sun ba da sanarwar ceto wasu mutane 90 daga hannun Boko Haram bayan da suka yi nasarar fatattakar su daga kauyukan Dissa da Balazala na cikin karamar hukumar Gwoza da ke Jihar Borno a yankin arewa maso gabashin kasar ta Najeriya
Mai magana da yawun sojojin kasar ta Najeriya Sani Usman ya bayyana cewa mutanen da suka yi nasarar cetowa a ranar Alhamis da ta gabata sun hada da maza 23 da mata 33 da yara kanana 34.
A shekarar da ta gabata kungiyar ta Boko Hram ta kaddamar da garin na Gwoza a matsayin babban birnin daular khalifancinta da ta yi ikirarin kafawa, kafin sojojin kasar su sake kwace birnin a cikin watan Maris da ya gabata.
Title :
An ceto mutane 90 daga hannun Boko Haram
Description : Hukumomin sojin Najeriya sun ceto wasu mutane 90 daga hannun kungiyar Boko Haram bayan da suka kori mayakan kungiyar daga kauyukan Dissa da ...
Rating :
5