Rahotanni daga Saudiyya na cewa yawan alhazan da suka mutu a hadarin da ya auku ranar Alhamis ya haura 1000 daya.
Alkaluman da hukumomin Saudiyya suka fara fitarwa dai na cewa sama da mutane 700 ne suka mutu.
Hukumar Alhazan Nigeria ta ce alhazanta 54 ne suka mutu, yayin da alhazai 61 suka jikkata.
Akwai dai alhazai da dama na Nijeriyar wadanda har yanzu ba a ji duriyarsu ba.
Buhari ya ba da umarnin tantance alhazai
Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, ya bukaci Hukumar aikin Hajji ta kasar da Ofishin Jakadancin kasar a Saudiyya da su gaggauta tantance 'yan Nijeriyar da wannan lamari ya shafa, domin a sanar da danginsu.
Hukumonin Nijar sun tabbatar da mutuwar alhazansu 22, yayin da ake ci gaba da bincike a kan sauran alhazan da suka bace bayan hadarin na Mina.
Title :
Alhazai fiye da 1000 ne suka rasu a Mina
Description : Rahotanni daga Saudiyya na cewa yawan alhazan da suka mutu a hadarin da ya auku ranar Alhamis ya haura 1000 daya. Alkaluman da hukumomin Sa...
Rating :
5