Bayanan da ake samu na baya-bayan ya nuna cewa alhazai 16 ne suka jikkata 10 kuma suka bata daga jihohin Plateau da Gombe da kuma Bauchi a turmutsitsin da ya faru a Saudiya
Alkaluman da BBC ta samu daga shugabannin hukumomin alhazai na jihohin uku na arewacin Najeriya a Makka, ya nuna cewa jihar Gombe na kan gaba da alhazai tara wadanda suka jikkata, biyar kuma suka bata.
A jihar Bauchi Alhaji daya ne ya rasu, hudu suka jikkata, wasu karin hudun suka bata. A jihar Pilato alhazai guda uku ne suka jikkata, daya kuma ya bata.
A cewar shugabannin hukumomin alhazzan an sallami dukkannin wadanda suka jikkata daga asibiti bayan an yi musu magani, sun kuma dukufa wajen neman wadanda suka bata.
Mutane fiye da 700 ne dai 'yan kasashe daban-daban aka tabbatar da mutuwarsu a hadarin da ya faru Mina ranar Alhamis kan hanyarsu ta zuwa jifar Shaidan.
Title :
Alhazai 16 na jihohi uku sun jikkata
Description : Bayanan da ake samu na baya-bayan ya nuna cewa alhazai 16 ne suka jikkata 10 kuma suka bata daga jihohin Plateau da Gombe da kuma Bauchi a t...
Rating :
5