Hukumomin Najeriya sun tabbatar da cewa akwai wasu 'yan kasar da suka mutu a hadarin ya afku a Mina inda sama da mahajjata 700 suka mutu sakamakon turereniyar da aka yi akan hanyar zuwa wurin jifan shaidan.
A hirarsu da BBC amirul hajji na Najeriya kuma sarkin Kano, Mai martaba Muhammadu Sanusi II shi ya ce har yanzu jami'an na Saudiya ba su gama tantance yawan mahajjatan kasar da abin ya shafa ba.
Haka shi ma ministan yada labarai na jamhuriyar Nijar Yahuza Sadisu Madobi ya ce akwai mahajjata daga Nijar wadanda lamarin ya shafa, sai dai har ya zuwa yanzu ba a tantance yawan wadanda suka mutu ko suka jikkata ba.
Mutane fiye da dari bakwai ne Allah ya yi wa cikawa a wani tirmutsitsi da aka samu a Mina a lokacin aikin Hajji.
Wasu daruruwan kuma sun samu raunika.
Jami'an Saudiyya sun ce al'amarin ya faru ne a Mina, a inda ake jifan shaidan.
Wakiliyar sashen Hausa na BBC, Tchima Illa Issoufou, ta bayyana cewa al'amarin ya rutsa da 'yan kasar Jamhuriyar Niger da dama.
Kawo yanzu babu takamaiman adadin yan Niger din da abun ya shafa.
A shekarun baya, an yi sha fuskantar turmutsitsi a wajen jifan shaidan, amma bayan wasu gyare gyare da mahukuntan saudiyya suka yi an samu sauki a yan shekarun nan.
Mutane fiye da miliyan biyu ne daga sassa daban daban na duniya suke halartar aikin hajjin na bana.
A farkon aikin hajjin na bana an fuskanci wani mummunan hatsari a lokacin da wata kugiya ta fadawa jama'a a Ka'aba inda mutane fiye da dari suka mutu.
Title :
'Da akwai 'yan Nigeria da Niger cikin wadanda suka mutu'
Description : Hukumomin Najeriya sun tabbatar da cewa akwai wasu 'yan kasar da suka mutu a hadarin ya afku a Mina inda sama da mahajjata 700 suka mutu...
Rating :
5