Fadar shugaban Nigeria ta fitar da sanarwa dake bayyana abubuwan da shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo suka mallaka kamar yadda suka gabatar ga hukumar tabbatar da da'a, wato Code of Conduct Bureau.
Sanarwar ta nuna shugaba Buhari ya mallaki kudi kasa da naira miliyan talatin kafin a rantsar da shi a matsayin shugaban kasa. Shugaba Buhari yana da asusun ajiyar banki daya, a Union Bank, amma ba shi da asusun ajiyar banki a kasashen waje, ko masana'anta.
Bayanan sun nuna shugaba Buhari ya mallaki gidaje biyu na kasa a Daura, daya ya gada daga marigayiya yayarsa dayan kuma daga mahaifinsa.
Kuma yana da gidaje biyu a Kaduna, da daya a Daura da daya a Kano da kuma daya a Abuja.
Sannan yana da filaye biyu daya a Kano daya kuma a Patakwal wanda kuma har yanzu yana kokarin gano inda yake.
Haka kuma yana da hannayen jari a kamfanonin Berger Paint, da bankin Skye, da kuma bankin Union.
Shugaba Buhari ya mallaki gonaki da shanu 270, da awaki 25, da dawaki 5.
Shi kuwa mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo ya mallaki abubuwan da suka hada da gida a unguwar Victoria Garden City da ke Lagos, da kuma wani gidan a unguwar Ikoyi a Lagos.
Yana da gida akan hanyar Lagos zuwa Ibadan mai daki biyu. Mataimakin shugaban kasar yana kuma da gida mai daki biyu a garin Bedford da ke Ingila.
Osinbajo ya kuma mallaki kudi kusan naira miliyan casa'in da hudu.
A baya dai an sha korafi dangane da jinkirin bayyana abubuwan da shugabannin suka mallaka.
Title :
Abubuwan da Buhari da Osinbajo suka mallaka
Description : Fadar shugaban Nigeria ta fitar da sanarwa dake bayyana abubuwan da shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo suka mall...
Rating :
5