Hakika duk wanda ya wayi gari cikin Imani da kuma yarda da hukuncin Allah, to ya samu babban arziki.
Wanda ya kiyaye harshensa daga Qarya da Qazafi, da Annamimanci da gulma, to hakika ya samu Babban tsaro. (Idan ka kiyaye harshenka daga chutar da mutane, Allah zai kiyaye mutuncinka awajen Mutane).
Wanda ya wayi gari zuciyarsa FES babu shirka, Babu Hassada, babu Qiyayya, babu Champi, babu Guluwwi babu Girman kai, babu Riya babu Sum'ah, to hakika ya kama igiyar Allah wacce ba zata tsinke ba.
Wanda ya samu Kyakkyawan Qarshe shine ya samu babban rabo.
Wanda ya rayu da lafiyayyar zuciya shine cikakken mai lafiya.. Idan kuma yaje ma Allah da ita ahakan, To zai samu lafiya ta har abadah wacce ba zata yanke ba.
Da yawa zaka ji mutum yana gaya maka Allah abakinsa, amma Zuciyarsa tafi mushe Wari.. Da za'a fidda zuciyarsa, ko karnuka ba zasu iya ci ba. Saboda mummunar Qazantar dake cikinta.
Da yawa zaka ga mutumin da bai kai komai acikin mutane ba, Ba'a sanshi ba ballantana a damu da sha'aninsa, amma Zuciyarsa tana tare da Allah.
Son Zuciya, Girman kai, Dogon buri, Hassada, da neman girma sune manyan cututtukan da suke damun mafiya yawanmu. Dole mu tashi tsaye mu nemi magani.
kowanne abu yana da soson da ake wankeshi dashi. Amma soson dake wanke Zuciya shine ZIKIRIN ALLAH (SWT).
DAGA ZAUREN FIQHU FACEBOOK.