Shugaban tawagar alhazan Nigeria kuma Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi na biyu ya bukaci hukumomi a Saudiyya su daina dora alhakin iftila'in da ya faru a kan mahajjata.
Turmutsitsin dai ya janyo rasuwar mutane kusan 717.
Hukumomi a Saudiyya sun zargi alhazai da kin bin umurni a kan hanyar zuwa jifan shaidan, abin da ya janyo aka samu hasarar rayuka.
"A daina bin hanyar da ba ta dace ba. Muna kira ga hukumomin Saudiyya su daina dora alhaki a kan mahajjata," in ji Sarki Sanusi.
Sarki Sanusi na biyu ya kuma bukaci alhazai su dinga bin umurni musamman a kan hanyoyin zuwa wuraren ibada.
Tuni dai Sarki Salman na Saudiyya ya bukaci a gudanar da cikakken bincike dangane da yadda hukumomin kasar ke gudanar da tsare-tsaren ayyukan Hajji.
Title :
A Daina Dora Alhaki A Kan Mahajjata - Sarkin Kano
Description : Shugaban tawagar alhazan Nigeria kuma Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi na biyu ya bukaci hukumomi a Saudiyya su daina dora alhakin iftil...
Rating :
5