Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta sake samun korafi na cin zarafin mata a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya wanda ake zargin jami'an kiyaye zaman lafiya na MINUSCA da yi.
Mai magana da yawun majalisar Vannina Maestracci ta shaidawa manema labarai dazu cewar wannan batu ya faru ne a 'yan makonnin da suka gabata, kuma iyalan wanda aka ciwa zarafin ne da kansu suka yi korafin.
Maestracci ta ce 'yan mata biyu da wata kankanuwar yarinya ce aka yi wa fyade sai dai ba ta bayyana suna ko kasar da sojojin da suka yi fyaden suka fito ba amma dai ta ce su uku ne.
A makon jiya sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya sallami shugaban rundunar ta MINUSCA Janar Babacar Gaye bayan da korafi kan zargin yi wa 'yan mata fyade ya yawaita.
Title :
Zargin fyade a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
Description : Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta sake samun korafi na cin zarafin mata a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya wanda ake zargin jami'an kiyaye za...
Rating :
5