Ma'aikatar lafiya a Masar ta ce matsanancin zafi ya janyo mutuwar mutane 61 a cikin kwanaki uku.
Lamarin ya yi kamari ne bayan da zafin ya kai ma'aunin selshiyos 47 (47C).
Kafar yada labarai ta gwamnati ya ce mutane 40 ne suka rasu a ranakun Lahadi da Litinin a yayinda 21 suka mutu a ranar Talata.
A halin yanzu akwai wasu mutane fiye da 581 da aka kwantar da su asibiti saboda gajiya tibis.
Yawancin wadanda suka rasu tsofaffi ne.
Title :
Zafi ya hallaka mutane 61 a Masar
Description : Ma'aikatar lafiya a Masar ta ce matsanancin zafi ya janyo mutuwar mutane 61 a cikin kwanaki uku. Lamarin ya yi kamari ne bayan da zafin...
Rating :
5