Shugaban kasar jamhuriyar Nijar Alhaji Mahammadou Issoufou, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta yi gaskiya da adalci a cikin zabubukan da za a yi a kasar a farkon shekara ta 2016.
Ya ce gwamnatinsa za ta baiwa kowane dan-kasa idan yana bukata, damar tsayawa takara a mukamin da yake so, ba tare da nuna masa wariya ko bambanci ba.
Shugaban kasar ya tabbatar da hakan ne a cikin jawabin da ya yi a ranar Lahadi, albarkacin bikin cikar shekaru 55 na samun 'yancin kan kasar, da ake yi ranar Litinin 3 ga watan Agusta.
Kazakalika, 'yan Nijar din mazauna Najeriya, 'yan jam'iyyar PNDS mai mulki, sun gudanar da wani taronsu a birnin Bauchi na arewacin Najeriya, kan shirye-shiryen zaben.
Hukumomin Nijar dai na daukar matakai domin ganin 'yan kasar da ke zaune a kasashen waje sun jefa kuri'a a inda suke, ba tare da sun koma gida ba.