Mai bai wa Shugaban Nigeria shawara kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya fadawa manema labarai cewa a karon farko Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya na fatan za a murkushe Boko Haram zuwa karshen shekara.
Shugaba Muhammadu Buhari ya furta hakan ne a ziyarar da ya kai zuwa Jamhuriyar Benin a ranar Asabar.
Ziyarar wani bangare ne na ci gaba da tuntubar shugabannin kasashe makwabtan Najeriya dangane da yadda za a shawo kan matsalolin tsaron da suke fama da su.
Malam Garba Shehu ya kuma fadawa manema labarai cewa Jamhuriyar Benin ta kuma sha alwashin taimakawa kasashen raya tafkin Chadi a yakin da suke yi da mayakan Boko Haram.
Jamhuriyar Benin ta ce zata ba da gudummuwar sojoji 800 domin wannan yaki