Najeriya wato NEMA ta gargadi al'ummomin da ke zaune a kusa da kogin Benue da su tashi domin akwai yiwuwar samun ambaliyar ruwa daga nan zuwa watan Nuwamba.
A wata sanarwa da kakakin hukumar ya fitar, Sani Datti, hukumar ta ce sun samu bayanai daga hukumomin jamhuriyar Kamaru cewa daga yanzu zuwa watan Nuwamban za a rinka sakin ruwa daga dam din Lagdo na kasar ta Kamaru saboda timbatsar da ya yi.
A Saboda haka ne hukumar ta yi kira ga mazauna yankunan da su kula.
Ta kuma kara da kira ga hukumomi da su kwashe mutanen.