Assalamu alaikum Allah Ya karawa Malam imani
Malam muna da tambaya kamar haka :
1 shin ya halatta ga macce matar aure ko maras aure tayi aikin karanta labari ko gabatar da Shirye-shirye a gidan television
Allah Ya bada ikon amsa mana
Allah Ya saka da alkairi
AMSA
*******
Gaskiya bai halatta ba. Ta fuskokinmu da dama. Musamman idan mun kalli irin Sheridan da addininmu ya gindaya ma Mata wadanda suka balaga, koda basu da aure. Ballantana kuma wacce take da aure.
1. FITA WAJE : Allah ya umurci Mata su zauna agidajensu. Kar su fita har sai idan akwai larura ko dalili MAI KARFI.
Allah yana cewa:
"KUMA KU ZAUNA AGIDAJENKU, KAR KUYI TABARRUJI IRIN TABARRUJIN NAN NA JAHILAN FARKO".
TABARRUJI : Shine Mace ta fita ba tare da cikakkun SUTURA masu kauri, masu lullubemu jiki ba.
Bayyanar da adonta, ko sanya Gayle, ko dangalallen Hijabi ko fesa turare wannan duk shima TABARRUJI ne.
2. CHAKUDUWA DA MAZAJEN DA BA MUHARRAMANTA BA: Wannan aikin da ka fada, babu yadda Mace zata yishi ba tare da ta chakuduwa da Mazaje ba.
Ko awajen neman labarai, ko a Ofishin Edita, dole sai ta kadaita da wani ko wasu wadanda ba MUHARRAMANTA ba.
Duk da Karfin imani irin na Sahabban Annabi (saww) Amma Allah ya hanasu suje kai tsaye suyi magana da Matansa.
Allah yace musu : "KUMA IDAN ZAKU TAMBAYESU WANI ABU, TO KU TAMBAYESU DAGA BAYAN HIJABI (TA BAYAN KATANGA KO LABULE).
3. BAYYNAR DA MURYARTA: Muryar Mace yana daga cikin abinda yakan jefa fitina acikin zukatan wasu Mazajen wadanda suke da raunin Imani a zukatansu. Shi yasa Allah yace ma Matayen Manzon Allah (saww) :
"KAR KU QAS DA MAGANARKU (WATO KAR KU SIRIRINTA MURYARKU IDAN ZAKUYI MAGANA DA MAZAJE) BALLANTANA WANDA KEDA CHUTA AZUCIYARSA YAYI KWADAYIN WANI ABU".
Ibnu Katheer yace haka Suddeey ya fassara ayar. Ibnu Zaidin kuma yace ma'anar ayar shine: "Kar Mace tayi magana da sauran mazaje da irin muryar da take magana da Mijinta. (Wato banda rangwada, ko kwarkwasa, da, sauransu).
To amma idan kun dubi yanayin aikin Jarida ba haka suke yi ba.
Bisa Qa'idarsu dole sai Mace ta koyi gwalagwalen Lafazi wadanda zata rika amfani dasu domin gabatar da Shirye shiryenta domin jan hankalin masu Kallonta ko masu saurarenta.
4. BAYYANAR DA FUSKARTA, HAR QIRJINTA: Dole ne mace idan zata gabatar da Labarai a Talabishan sai ta bayyanar da Fuskarta a fili, kuma sai ya zama ana iya ganin Qirjinta ma.
Wannan Haramun ne bisa ittifakin dukkan Maluman Musulunci. Duk da cewa Hadisi ya nuna cewar "MACE DUKKANINTA AL'AURA CE. AMMA BANDA FUSKA DA KUMA TAFIN HANNUWA".
To amma ana nufin Matar da kallonta ba zai zama fitina ba. Amma duk Matar da kallonta zai iya jefa fitina azukatan mazaje, to bai halatta ta rika bayyanar da fuskarta a ko ina ba. Kuma koda Masallacin Eidi ko Jam'in salloli a Masallaci ance kar ta je.
To amma aikin karanta Labarai a Talabishan wata hanya ce wacce ita matar take bayyana kyawunta ga Mazaje. Hasali ma sai ta chaba ado, ta sanya Qayatattun Tufafi sannan tazo ta zauna don karanta labaran.
Musulunci ya yarda mace ta fita tayi aikin Gwamnati amma bisa ka'idodi masu yawa kamar haka:
1. Ya zamto akwai larura babba wacce ta haddasa mata yin aiki. kamar Misali idan batta da mai ciyar da ita, ko daukar nauyin Yaranta ko iyayenta tsofafgi masu rauni.
2. Wajibi ne aikin ya zama irin wanda ya dace da mata ne. Misali kamar Aikin Likita, ko Jinya (nurse) ko karbar haihuwa, ko Sakar tufafi, etc.
Ko kuma koyar da Wasu matan ko Qananan yara wadanda basu balaga ba.
3. Dole be ya zamto babu chakuduwa tsakanin Maza da mata awajen aikin.
4. Dole be ta zamanto sabye da cikakkiyar Suturar kamala tun daga gida har akan hanyar tafiya wajen aikin, kuma har awajen aikin ma.
5. Kada aikin ya janyo mata yin tafiya ba tare da Muharrami ba.
6. Dole ne ya zamto bata kadaituwa da wani namijj koda Direba ne ayayin tafiyarta wajen aikin. Kuma kar ta fesa turare ko bayyanar da adonta.
7. Dole be ya zamto aikin nata ba zai janyo mata dalilin da zatayi sakaci da Muhimman ayyukanta ba. Misali kamar kulawa da mijinta, ko 'ya'yanta, ki kuma gidanta.