Yin afuwa ga mutumin da ya zalunceka yana daga cikin halaye ko dabi'o'i masu wahalar aiwatarwa. Amma kuma yana daga cikin dabi'un manyan Annabawa da Manzanni (as).
Manzon Allah (saww) ya fada acikin Hadisin da Imamu Muslim ya ruwaito daga Abu Hurairah (as) :
"DUKIYA BA ZATA TA'BA TAUYEWA SABODA SADAQAH BA, KUMA ALLAH BA ZAI QARA MA BAWA KOMAI TA DALILIN YIN AFUWA BA, SAI DAI IZZAH (WATO GIRMA). KUMA BABU WANI MUTUMIN DA ZAI QASKANTAR DA KANSA DOMIN ALLAH, FACHE SAI ALLAH YA DAUKAKASHI".
Awani Hadisin kuma Manzon Allah (saww) yace: "WANDS YA IYA KOKUWA BA SHINE MAI KARFI BA. MAI KARFI SHINE WANDA YAKE IYA MALLAKAR ZUCIYARSA YAYIN BACIN RAI".
(Bukhary da Muslim ne suka ruwaitoshi).
Awani wajen kuma Manzon Allah (saww) yace: "BABU WANI MUTUM WANDA ZAI HADIYE FUSHI ALHALI YANA DA IKON AIWATAR DASHI (WATO DAUKAR FANSA) FACHE SAI ARANAR ALKIYAMAH ALLAH YASA AYI KIRANSA YA SHIGA ALJANNAH TA INDA DUK YASO".
Da wannan nake Qara jan hankalin 'Yan uwa musulmai cewa mu rika kokarin aiki da dukkan abinda muka karanta, ba wai mu karanta mu wuce ba.... A'a mu shigar da karatun nan acikin Mu'amalar mu da iyalanmu, da abokanmu, da iyayenmu, da 'ya'yannu, da ma'aikatanmu da dukkan wadanda ke tare damu. Har ma Mutanen da bamu sansu ba..
DAGA ZAUREN FIQHU .