A Najeriya, a ranar Alhamis ne ake cika kwanaki 500 tun da 'yan kungiyar Boko Haram suka sace 'yan matan makarantar Chibok fiye da 200 da ke jihar Borno.
Masu fafitikar ganin an ceto 'yan matan, karkashin kungiyar #BringBackOurGirls, sun sha alwashin gudanar da taruka daban-daban a ranar ta Alhamis domin jaddada bukatarsu ta ganin an ceto 'yan matan.
A watan Afrilun shekarar 2014 'yan Boko Haram suka je makarantar Chibok da tsakar dare suka sace matan, lamarin da ya ja hankalin kasashen duniya.
A wancan lokacin, Shugaban kasar Goodluck Jonathan ya sha suka daga al'umar duniya saboda rashin katabus wajen ceto 'yan matan.
Gwamnatinsa ta sha cewa masu fafitikar ganin an ceto 'yan matan suna yi ne da zummar bata mata suna, zargin da suka sha musantawa.
Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ya hau karagar mulki a watan Mayun shekarar 2015, ya ce zai yi kokarin ceto 'yan matan, sai dai 'yan kungiyar ta #BringBackOurGirls ta bukace shi ya gaggauta aiwatar da aniyarsa ta ceto 'yan matan.
Title :
Yau Kwana 500 Da Sace 'Yan Matan Chibok
Description : A Najeriya, a ranar Alhamis ne ake cika kwanaki 500 tun da 'yan kungiyar Boko Haram suka sace 'yan matan makarantar Chibok fiye da 2...
Rating :
5