Dakta Fatima Atiku, ‘yar Tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar ta samu mukamin Kwamishiniyar lafiya a jihar Adamawa, ta zama cikin jerin sunayen Kwamishinoni 22 da Gwamnan jihar, Bidow Jibrilla ya aike zauren Majalisar Dokoki domin tantancerwa.
Haka kuma, biyu daga cikin na kusa da Atiku Abubakar, Ibrahim Yayaji Mijinyawa, wanda ya tsaya takarar fidda gwanin a kujerar Gwamna a APC, da Umar Diya Daware duk sun samu mukamin Kwamishinan.
Haka zalika, Tsohon Daraktan yada labaran Tsohon Gwamna Nyako, Ahmad Sojo, shi ma yana daga cikin jerin sunayen sabbin Kwamishinonin, da kuma tsaffin Kwamishinoni biyu a lokacin Nyako, Muhammad Barkindo Aliyu Mustafa da Lilian Nabe Kayode.
Haka kuma akwai mata hudu daga cikin jerin sunayen Kwamishinonin 22 da Gwamna Bindow Jibrilla ya aike wa Majalisar Dokokin, wadanda suka hada da Shanti Bictoria, Kaletapwa Farauta, Fatima Atiku da kuma Lilian Nabe Kayode.
Tuni dai zaman Majalisar na ranar Alhamis ta makon jiya ya tantace Kwamishinoni 12 daga 22 da Gwamna Bindow Jibrilla ya aike masu.
Title :
Yar Atiku Abubakar Ta Samu Mukami
Description : Dakta Fatima Atiku, ‘yar Tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar ta samu mukamin Kwamishiniyar lafiya a jihar Adamawa, ta zama cikin...
Rating :
5