Hukumomin kasar Masar sun ce tsananin zafin rana ya hallaka mutane 21 da kuma kwantar da sama da 66 a asibiti. Zafin mai maki 47 a ma’aunin celcius, shine irin sa na farko a tsawon shekaru da a yanzu ke tayiwa mutane kasar illa.
A sanarwar da ta fitar ma’aikatar lafiyar kasar ta ce 15 daga cikin wanda suka mutu mazauna birinin cairo ne, raguwan kuma mazauna yankin Marsa Matruh da Qena.
Sanarwar ta kuma kara da cewa 7 daga cikin wadanda suka mutu tsofafin mata ne da shekarunsu ya haura 60 a duniya, kuma a halin da ake ciki yanzu akwai wasu mutane 37 da ke can rai a hannu Allah.
Yanayin zafin a bana ya tsananta a masar sama da shekarun baya, wanda hucinsa ke Jefa mutane a cikin wani yanayi.
Masu hasashen yanayi a kasar sun ce yanayin zafin bana ya karu da maki 5, wanda ba a saba da shi ba.
Tuni dai Mai Magana da yawun ma’aikatar lafiyar kasar Hossam Abdel Ghaffar ya gargadi al’ummar kasar da su gujewa daukan tsawon lokaci a cikin ranar saboda illar ta.
Title :
Yanayin zafin rana mai tsananin na kashe mutane a Masar
Description : Hukumomin kasar Masar sun ce tsananin zafin rana ya hallaka mutane 21 da kuma kwantar da sama da 66 a asibiti. Zafin mai maki 47 a ma’aunin ...
Rating :
5