Ofishin huddar jakadancin kasar Saudi Arabia a birnin London ya tabbatar da cewa dangin marigayi shugaban kungiyar al-Qaeda,Osama bin Laden sun hallaka a wani hadarin jirgin sama a kudancin Ingila.
Jakadan kasar ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan bin Laden, amma kuma bai bayyana ainihin ko su wanene ba.
'Yan sanda sun ce mutane hudu da suka hada da matukin jirgin ne ke cikin karamin jirgin mai lambar kasar Saudia, lokacin da ya subuto kasa a ranar Jumma'a kana ya kama da wuta.
Ofishin huddar jakadancin ya ce zai yi aiki tare da masu bincike na kasar Birtaniya, don tabbatar da an kai gawwaakin gida Saudi Arabia don yi musu jana'iza.