Yan APC dake kasashen Scandinavia sun bada wani gargadi akan wadanda suke sukar yaki da rashawar da shugaba Buhari yakeyi.
Ko’odinatan kasar, Ayoola Lawal ya bayyana cewa abun takaici ne ace yaki da rashawar da shugaba Buhari yake yi bata lokaci ne.
Yace: ”A dubar data dace, yaki da rashawa da akeyi ba bata lokaci bane. Ba kuma musanta aikin daya dace bane. Idan dai har abunda wasu suke gani cewa bata lokaci ne zaya kawo mutunci da kuma bin doka da tsari, toh wannan zaya zama mafi girman romon Damakaradiyya da najeriya ta taba samu.”
Ko’odinatan kuma ya nuna rashin amincewar shi akan yadda wasu manyan kasa ke kokarin hana binciken amma kuma basu hana na barayin gwamnati yin sata ba.
Title :
Yan Najeriya Sun Goyi Bayan Buhari
Description : Yan APC dake kasashen Scandinavia sun bada wani gargadi akan wadanda suke sukar yaki da rashawar da shugaba Buhari yakeyi. Ko’odinatan kasa...
Rating :
5