Masu aikin ceto a tekun Bahar rum sun ce suna fargabar an rasa rayuka da dama bayan wani jirgin ruwa ya nutse a kusa da kasar Libya.
Rahotanni sun ce ana kyautata zaton a kalla mutane 700 ne a cikin jirgin.
Masu tsaron tekun Italiya, wadanda ke jagorantar ceton, sun ce a halin da ake ciki yanzu kusan mutane 400 ne aka ceto.
Jirgin kama kifin ya samu matsala ne kilomita 25 daga tasowar ta daga bakin tekun Libiya, sakamakon sauyin yanayi mai tsanani da aka samu, inda nan da nan ta tura sakon neman taimako ga garin Sicily.
Akalla jiragen ruwa hudu da jirage masu saukar ungulu uku ne suka isa wurin domin aikin ceton.
Jirgin ya kife ne kuma sakamakon tattarewa a gefe guda da 'yan ci-ranin suka yi a lokacin da suka ga tahowar masu aikin ceton.
'Yan ci-rani sama da 2,000 ake zaton sun nutse wannan shekarar, a yunkurin tsallaka tekun zuwa Turai.