Dubun daubatan mutanen rikicin Boko Haram ya daidaita. Taimakon da gwamnati da wasu kungiyoyi suka shirya na tallafa masu wasu na ji ne kawai basu gani a kasa ba.
Kafin hare-haren 'yan Boko Haram, Gata dake yankin Michika a arewacin jihar gari ne dake da hada hadar kasuwanci da ayyukan sufuri lamarin da 'yan Boko Haram suka tarwatsa.
Wasu 'yan jarida tare da wakilin Muryar Amurka sun leka garin domin gani da ido.
Sun tarar da al'ummar garin cikin wani mawuyacin hali da kuma rashin samun tallafi.
Alhaji Baba Muhammad da Peter Zira mazauna garin ne. Irin wadannan mutanen ba zasu taba mantawa da azabar da suka sha ba kuma har yanzu suna kan sha.
Alhaji Muhammad yace yana cikin halin kunci saboda duk wani taimako da aka ce gwamnati na bayarwa basu gani a kasa ba. Bugu da kari garinsu ne ya fi samun yawan hare-hare daga Boko Haram. Cikinsu ne aka yiwa mutane fiye da 20 yankan rago banda gidaje fiye da dari da aka kone.
Wadanda suka gudu zuwa Kamaru an korosu sun kwashe kusan wata daya cikin duwatsu.
Kawo yanzu babu wani taimako daga ko hukumar bada agajin gaggawa wato NEMA ko daga bankin duniya.
Mutanen garin na bukatar gwamnati ta basu tsaro da taimako. Sun kira gwamnati ta bincika abun da suke fadawa 'yan jarida.
Title :
Yan Binidga Sun Kashe Sojoji Da Dansanda A Jihar Bayelsa
Description : Dubun daubatan mutanen rikicin Boko Haram ya daidaita. Taimakon da gwamnati da wasu kungiyoyi suka shirya na tallafa masu wasu na ji ne kawa...
Rating :
5