Rahotanni na cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari a wajen binciken abababen hawa a Nembe a jihar Bayelsa sun kuma hallaka sojoji hudu.
'Yan bindigar sun kuma dauke makaman su, wadanda suka hada da kananan bindigoi da kuma wata bindiga mai sarrafa kanta wacce aka girke a wurin.
Laftanar Kanar Ado shugaban rundunar tsaro ta JTF ya tabbatar da labarin kai harin ga wakilin manema labarai amma bai ce komai ba game da kashe sojojin.
Babu kungiyar da ta dauki alhakkin kai harin.
A baya dai yankin na Niger Delta mai arzikin mai ya sha fama da hare-hare daga 'yan kungiyar fafutuka ta yankin masu gwagwarmaya da makamai