Cacar baki tsakanin gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai da Sanata Shehu Sani mai wakiltar shiya ta biyu na kara yin tsamari
Magoya bayan kowane bangare na cigaba da jifan juna da kalamu masu tada rai.
Alhaji Ahmed Suleiman mai baiwa sanata Sani shawara akan harkokin siyasa yace karta layi tsakanin mutanen biyu ba yau ya fara ba.
Yace Sanata Sani ya banbanta da sauran zababbu. Duk wanda ya san Shehu Sani ya san mutum ne mai gwagwarmaya da zafi musamman akan abun da ya shafi al'umma.
Rushe-rushen da gwamna ya fara bai fara kan ka'ida ba. Maimakon gwamnan ya fuskanci abubuwan da suka yiwa mutane katutu a rayuwarsu ya kama rushe gidaje wai domin ba'a ginasu kan ka'ida ba. A bangaren Sani ana ganin kuskure ne babba.
Duk da cewa filayen na gwamnati ne amma gwamnatin ce ta basu. Babu wanda zai dauki fili kawai ya fara gina gida a kai bada izinin gwamnati ba. Idan an basu ne bisa kuskure rushesu ba shi ne gyara ba.
Amma magoya bayan gwamnan irinsu Alhaji Ibrahim Jumare nada ra'ayin cewa gyaran da gwamnan yake yi nada kyau kuma duk lokacin da aka so yin gyara dole ne wasu ba zasu ji dadi ba.
Alhaji Jumare yace ya goyi baya domin makarantu da aka kwace filayensu aka gina gidaje. Makarantu haki ne na jama'a saboda haka kamata yayi a kwato filayen. Abun mamaki cikin makarantu aka shiga aka yi gine-ginen. Makarantu kuma mallakar gwamnati kuma kayan jama'a ne.
A taimaki gwamnan da addu'a ba a soma zarginsa ba. Dole ne a kawar da barna kafin a kawo maganin barna.