Fatima: Ni dai an haife ni a garin Kano, kuma a nan na girma. Na yi digirina na farko a jamia’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Daga nan kuma na samu tallafin kudin karo karatu daga gwamnatin jahar Kano a lokacin gwanan Kano Rabi’u Kwankwaso, domin na karanta yadda ake tukin Jirgin-Sama a kasar Jordan. Na samu kimanin shekaru biyu sannan na kammala wannan karatu, a yanzu na samu lisisin tuka Jirgin-sama.
Aminiya: Me ya ba ki sha’awa har kika tsunduma cikin karatun koyan tukin jirgin sama, musamman kasancewarki bahaushiy ‘yar Arewa mutuniyar jahar Kano?
Fatima: To shi dai jirgin sama wani abu ne maI ban sha’awa da ban alajabi. A duk lokacin da na ga jirgi a sararin samaniya na kan yi mamaki na kan tambayi kaina, to mene ne yake tafiyar da shi a sama ba tare da ya fado ba? Shin wai ta yaya masu tuka shi suke sarrafa na’urorinsa?
Wannan tunani da kwadayin sanin amsoshin wadanna tambayoyi nawa ya sa na tsunduma wajan bincike musamman a yanar gizo, wato wadda ake kira internet da turanci, a kan Jirgin sama da yadda ake sarrafa shi. Tun daga nan kuma na ji ba ni da wani buri face in koyi tukin jirgin sama.
Tukin jirgin-sama abu ne da yake bukatar abubuwa da dama. Yana bukatar karatu da nutsuwa da himma da kuma kwazo. Saboda haka ba za a ce lalle sai namiji ne zai yi tukin jirgi ba, a dakin karatu duka abu iri daya ne ake koyarwa ga mazan da matan babu wani bambanci. Saboda haka duk wanda ya maida hankali ba wani abu ba ne wanda ze gagara.
Aminiya: Wane irin kalubale kika fuskanta lokacin da kika fara koyan tukin jirgin sama?
Fatima: Gaskiya ba zan iya cewa na fuskanci wani kalubale ba a lokacin da na fara wannan karatu ko kadan, kamar yadda na fada in dai mutum zai dage abu ne da ba zai gagara ba.
Aminiya: To a matsayinki na mace fa a lokacin da ki ke wannan karatun?
Fatima: E!!! to!!!, na bar gida zuwa garin da ba nawa ba, ba ni da kowa a can kuma ban san kowa ba. Na samu kaina a cikin mutanen da ba kalarmu daya ba, ba yarenmu daya ba. Kasancewar ni kadai ce mace a cikin maza dari wani abin damuwa ne, amma hakan bai sa na karaya ba. A haka na daure na jajirce, kuma Alhmdlillah, Allah Ya sa na yi nasara a kan dukan jarabawa da gwaje-gwajen da aka yi min a cikin jirgi, musamman wurin tashi da sauka. Ina godiya ga Allah (S.W.T) da Ya cika min burina har na kammala wanan karatu na samu lasisin tukin jirgin sama.
Aminiya: Akwai wani jirgi na musamman da kawai shi ne za ki iya tukawa, ko kuwa duk wani irin Jirgin sama za ki iya keta hazo da shi?
Fatima: Kowane matukin jirgi da kake gani akwai irin jirgin da ya kware a kai. Ba Kowane jirgi ne kake da ikon tukawa ba, sai dai wanda ka yi karatun kwarewa a kan shi, kuma kake da lasisin tuka shi. Misali, akwai jirgi kirar boeing 747 mai daukar kimanin fasinja dari biyar, akwai irinsu da yawa manya da kanana sai wanda mutum yake da ra’ayin ya yi kwas a kai ya samu lasisin tuka shi.
Aminiya: Ya kika ji a lokacin da kika fara zama a gaban jirgi a matsayin ki na mai tuki?
Fatimah: Na ji wani irin farin ciki wanda ban taba ji ba, sai na ga kamar ina mafarki ne wanda ba na so in tashi daga barcin.
Aminiya: To lokacin da kika jiki kina kutsawa cikin hazo fa me ya faru?
Fatimah: ina samun kaina ina mai cike da farin ciki da nishadi a kodayaushe nake tukin jirgi, musamman ma idan ni kadai ce nake tukin ba tare da me koyarwa ba.
Aminiya: Ku nawa ne mata ‘yan Kano kuka kammala wannan karatun?
Fatymah: Gaskiya ni kadai ce mace ‘yar jihar Kano.
Aminiya: Yanzu da kika gama wannan karatu meye burinki, kina so ne ki dinga tukin ko kuma za ki shiga aji ne kina koyarwa?
Fatima: kwarai kuwa, ina da burin in fara tuka baban jirgi na daukar fasinja nan ba da dadewa ba in Allah Ya yarda.
Aminiya: Shin kina ganin mace mai aure za ta iya rungumar tukin Jirgin-sama?
Fatimah: Sosai kuwa. Akwai mata da dama a kudancin Nijeriya da nahiyoyin Afrika da Turai matuka jirgin sama kuma suna da aurensu da iyalansu sosai.
Title :
Yadda na ji ranar da na fara tuka jirgin sama -Fatima Gwadabe
Description : Fatima: Ni dai an haife ni a garin Kano, kuma a nan na girma. Na yi digirina na farko a jamia’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Daga nan kuma na...
Rating :
5