Daga: Marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam
[Rahimahullah].
(Malam ya yi wannan bayanin ne a Tafsirin Maiduguri
na shekarar 2006M a cikin Suratut-Taubah aya ta 100)
“Wankan Janaba yana da siffa guda biyu: Akwai
'siffatul ijza' (ta wadatar), kuma wacce ake kira 'siffatu
kamal' (ta kamala).
Wankan Janaba a siffar sa ta kamala shi ne: Idan ka zo
za ka yi ko za kiyi wanka ga ruwa a gabanka. Farkon
abin da za ka fara yi shi ne:
Za ka karkato bakin mazubin ruwanka, ka wanke
hannunka sau uku, sannan sai ka tsoma hannu a cikin
ruwan sai ka debo ka wanke gabanka, a dai-dai lokacin
da za ka wanke gabanka a lokacin za ka kulla niyya ta
wankan Janaba (Ko waninsa) wanda yake wajibi ne,
idan ka wanke gabanka ma'ana ka yi tsarki kenan, to
daga nan kuma sai ka yi alwala irin yanda kake alwala
ta sallah, abin da duk kake a alwala ta sallah za kayi
sai abu daya shi ne wanke kafafu to wannan za ka
kyale shi ba za kayi shi ba, to daga nan sai ka tsoma
hannunka guda biyu a cikin ruwan ba tare da ka debo
ruwa ba sai ka murmurza kanka saboda kowane gashi
da ya bude a lokacin da maniyyi yake kokarin fita
daga jikinka ya koma yanda yake, don gashin dan
Adam yakan bude musammam gashin sa na ka, idan
ka zuba ruwa a haka na iya haifar maka da ciwon kai
ko wani abu daban, bayan haka sai ka debi ruwa a
cikin tafin hannunka daya sai ka zuba a kanka ka
tabbatar ya game ko ina a kanka, ka sake kanfata na
biyu ka tabbatar ya game ko ina a kanka, haka na uku
ka tabbatar ya game ko ina a kanka.
To idan ka yi wannan sai ka debi ruwa ka game
dukkanin jikinka da shi kana mai farawa da bangaren
jikin ka na dama kafin na hagu, sannan na hagu ka
tabbatar ruwa ya taba ko ina. To idan ka yi wannan ne
ka kammala, abu na karshe shi ne sai ka wanke
kafarka ta dama sannan kafarka ta hagu shi ne cikon
alwalar da ka riga ka faro. Wannan ita ce siffa ta
kamala a wankan Janaba.
In wankan Janaba ne haka za ka yi, in na Haila ne haka
za a yi in ma wanka ne na Biki haka mace za ta yi,
idan wankan Jumu'a ne ma haka za a yi, wankan Idi
ma haka za ka yi, banbanci kawai shi ne NIYYA.
Idan mutum zai yi siffa ta 'Al ijza' wadda ta wadatar
ba sai ka yi alawa a cikin ta ba, kana zuwa ka yi niyyar
yin wanka din kawai sai ka dauki ruwan ka watsa a
jikin ka ya game ko'ina, in ma wani kududdufi ne ko
rami ko “swimming pool” sai ka yi tsalle ka fada a ciki,
dama ka kulla niyyar ka kafin ka shiga, daga ka fito
abin da za ka yi shi ne abubuwa guda biyu, kurkurar
baki da kuma shaka ruwa a hanci da fyacewa. Shi
kenan, kuma ya halatta ka yi sallah da wannan
wankan, Hadisi cikin Sahihu Muslim ya nuna haka.
Sai dai wanda ya yi wanka na farko ya fi ka kamala
saboda ya bi dukkan sharuddan, ya fi ka cikar kamala,
ya fi ka lada.
Kasancewar ba a yi alwala ba ciki, wannan ka'ida ce ta
malamai cewa karamin kari (HADATHUL ASGAR) idan
sun hadu da babban kari (HADATHUL AKBAR) to da ka
kawar da babban kari, karamin ma ya tafi. Amma ba
lallai bane idan ka kawar da karamin a ce babban ma
ya tafi."
Wani bawan Allah ne ya rubuta wannan, Allah ya saka
ma sa da alkhayri. Ameeen.