Assalam alaikum Mallam Allah yakara lafiya da Nisan kwana......Dan Allah mallam wani abokina ne ya kirani yake tambayata akan ya karbi wayar abokinsa zai tura wadansu Application amma yana dubawa sai yaga wayansu hotunan batsa ko kuma chatting na batsa Wanda hakan ne yasa har yayi releasing wato ya fitar da maniyyi to wai Dan ALLAH mallam meye hukuncin azuminsa???
Dan Allah aduba Tambayata wacce naturo tun cikin azumi, sabida yana son ya sani kaffara zaiyi ko ko dai ciyarwa zaiyi? Sannan idan ciyarwa ne ta yaya zai kasance? wato tayaya zai ciyar da mabukatan? Allah yakara basira da hasken karatu Amin.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Hakika wannan abokin naka ya aikata babban kuskure. daga cikin manyan laifukan da ya aikata akwai:
1. Keta alfarmar watan Ramadhan din.
2. Kallon abinda Allah ya haramta masa.
3. Ganganci karya azuminsa.
Da farko akwai bukatar ya tuba zuwa ga Allah (SWT) bisa wannan laifin da ya aikata. Sannan kuma Hukuncinsa shine zai yi ramukon azumin wannan ranar ne kawai. babu kaffara akansa.
WALLAHU A'ALAM.