Tun azamanin Manzon Allah (saww) an samu rikici tsakanin Muminan Aljanu da kuma kafiran cikinsu dangane da wuraren zama. Sai Manzon Allah (saww) ya zaunar da Muminan cikinsu akan tuddai da duwatsu, su kuma Kafiran ya zaunar dasu a kwarurruka da kwazazzabai.
Abinda bincike ya nuna shine, Muminan Aljanu sun fi son zama a wuraren da babu kowa, Wuraren da 'Dan Adam bai cika zuwa ba. Saboda suna gudun faruwar wani abu wanda zai kawo chutarwa tsakaninsu da 'Dan Adam.
Amma su kafiran cikinsu, sun fi son zama aguraren Qazanta da wari, da duhu. Misali kamar:
1. Ban-Daki (bathrooms).
2. Public Toilet (gidajen wanka).
3. Wuraren zubar da shara (bola).
4. Kwatammi (Sewage).
5. Mayanka (wato kwata, ko kuma wajen Yanka dabbobi).
6. Kufayi (rusassun gidajen da babu kowa.
Hakanan akwai kuma da yawa daga cikin Muminai da kafiran Aljanu wadanda suke zaune acikin garuruwan Bil Adam. Ana harkoki tare dasu.