Dan wasan Arsenal Jack Wilshere ya ji rauni a kafarsa lamarin da ka iya tilasta masa yin jinya ta makonni shida zuwa takwas.
Dan wasan, mai shekaru 23, ya yi raunin ne a lokacin da yake atisaye ranar Asabar , kwana daya kafin wasan da Arsenal ta doke Chelsea da 1-0 a gasar Community Shield.
Ba za a yi masa tiyata sakamakon raunin ba, sai dai ana sa ran ba zai buga wasannin ba tsawon watanni biyu a kakar wasa ta bana.
A kakar wasan da ta wuce, Wilshere ya kwashe watanni biyar bai taka leda ba sakamakon raunin da ya yi a idon sawunsa.
An yi masa tiyata sau biyu a idon sawun nasa a watan Nuwamba, kuma ya koma taka leda inda ya buga wasanni shida na karshe da kungiyar, cikinsu har da wasan karshe na gasar cin kofin FA na Ingila da suka fafata da Aston Villa.
A watan Yuni, Wilshere ya buga wasan sada zumuncin da Ingila ta yi kunnen-doki da Jamhuriyar Ireland, da kuma wasan da suka yi nasara a kan Slovenia a wasan neman shiga gasar cin kofin Turai.
Dan wasan ya sha yin fama da rauni tun da ya shiga fagen tamaula, kuma yawancin raunukan yana yin su ne a idon sawu.
Title :
Wilshere Ya Tafi Injuri Sati Takwas
Description : Dan wasan Arsenal Jack Wilshere ya ji rauni a kafarsa lamarin da ka iya tilasta masa yin jinya ta makonni shida zuwa takwas. Dan wasan, mai...
Rating :
5