Watarana Sayyiduna Umar bn Khattab (ra) Sarkin Muminai ya hau Mimbari yayi ma mutane Khutbah, ya bukacesu da cewa kar su rika zurfafawa Wajen biyan sadakin matayensu. yace tunda Manzon Allah (saww) da Sahabbansa bassu biyan sama da dirhami dari hudu. Don haka yace kar mutane su rika wuce wannan adadin kudin idan zasu biya sadaki.
Bayan ya gama Hudubar ya sauko daga Minbari sai wata Mata Bakuraishiya mai hikima tace masa: "Ya kai Sarkin Muminai shin kai ne kace kar Mutane su rika biyan sadaki fiye da dirhami dari hudu?" Sai yace mata "Eh nine".
Sai tace masa: "Shin baka ji (Acikin Alqur'ani) wajen da Allah yake cewa "Kuma kun bama wata daga cikinsu dukiya mai yawa" bane? (Wato Allah da kansa ya ambaci sadaki da sunan Qintaar. Wato dukiya mai yawa).
Da Umar yaji haka sai yace: "Ina neman gafararka Ya Allah. Dukkan Mutane sun fi Umaru Ilimi".
Sai ya koma ya hau Minbari yace ma Mutane "Na kasance ina cewa kar ku bada sadaki fiye da Dirhami 400, to amma daga yanzu duk wanda yaga dama ya bayar da duk abinda yaso".
DARASI
*********
Darussan da suke cikin wannan Qissar suna da yawa. Amma daga ciki akwai:
1. Yin ladabi ga Shugabanni. wannan matar batayi masa magana alokacin da yake jan minbari ba. sai bayan ya sauko sannan ta tuntubeshi tayi masa magana cikin ladabi.
2. Adalci irin na Shugabanni: Sayyiduna Umar yayi. aganar ne don neman saukaka ma al'ummah.
3. TAWADHU'U (RASHIN GIRMAN KAI) : Da ache irin shugabannin zamanin nan ne, Wani talaka Qasa dasu bai isa ya gyara musu abu, kuma suyi aiki dashi nan take ba.
Da fatan Allah shi amfanar damu da abinda muka