Wani matashi dan asalin kasar Morocco dauke da bindiga ya jikkata mutane biyu a cikin wani jirgin kasa daya taso daga Amsterdam zuwa birnin Paris na kasar Faransa bayan ya bude wuta a dai dai lokacin da Jirgin ke ganiyar gudu.
Mai Magana da yawun kamfanin jiragen kasa na Faransa ya ce wasu fasinjoji biyu 'yan Kasar Amurka ne suka ci karfin matashin kuma tuni ya shiga hannun jami’an tsaro.
To sai dai kawo yanzu, ba a gano dalillin da yasa dan bindijgan ya kai harin ba yayin da masu shigar da kara na Kasar ta Faransa suka ce, kwararru a fannin binciken ayyukan ta’addaci sun fara gudanar da bincike kan lamarin.
Ministan Harkokin cikin gida na Faransa Bernard Cazeneuve na kan hanyar sa ta zuwa yankin garin Arras a daidai inda lamarin ya auku.
Title :
Wani matashi ya kai hari cikin jirgin kasa a Faransa
Description : Wani matashi dan asalin kasar Morocco dauke da bindiga ya jikkata mutane biyu a cikin wani jirgin kasa daya taso daga Amsterdam zuwa birnin...
Rating :
5