Masu mu'amala da shafin sada zumunta na Twitter sun yi tsokaci sosai a kan wata sabuwar wakar da jarumin fina finan Hausa, Sani Danja ke shirin kaddamarwa.
Wakar, mai suna As E Dey Do Me a turance, ta dauki hankali ma'abota shafin sada zumuntar ne saboda an yi amfani da harshen Hausa da Turanci a cikinta.
Sani Danja ya shaidawa BBC cewa wakar ta yi masa bazata, yana mai cewa bai yi tsammaci za ta ja hankalin jam'a haka ba.
Wakar dai ta fi karkata ne ga turanci maimakon Hausa, amma mawakin ya ce idan kana son ka karbu a wurin masu saurare ka kan tafi ne a hankali, da ka karbu a inda kake so to za ka iya amfani da harshen aka zalla kuma mutane za su karbi abin hannu bibbiyu ba tare da duba ga harshe ba.
A cikin wakar, Sani Danja ya bukaci masu saurarensa su dogara ga Allah, yana mai cewa duk wata hanya da mutum ya bi idan ba ta ubangiji ba ce ba ta bullewa.
Wasu dai na ganin yawancin wakokin Sani Danja ba sa nuna al'adun Bahaushe, musamman ta fuskar suruta da kalami.
Sai dai mawakin ya musanta hakan, yana mai cewae ba sutura ce a bar kallo ba darasin da wakar ta kunsa shi ne mai muhimmanci.
Ya kara da cewa wasu daga cikin wakokin da ya yi da takwarorinsa da ke kudancin Nigeria sun kwaikwayi suturar Hausawa, misali babbar riga da hula.
Title :
Wakar Sani Danja ta ja hankali a Twitter
Description : Masu mu'amala da shafin sada zumunta na Twitter sun yi tsokaci sosai a kan wata sabuwar wakar da jarumin fina finan Hausa, Sani Danja ke...
Rating :
5