Assalamu alaikum Da fatan Allah ya saka wa Malam da alhkairi, ameen.
Malam ina da wata yar tambaya kamar haka: Malam ya dace mutum yasa ayi mashi rokon Allah kan wani mutum domin yasamu wani abu?.Akwai maigidana muna tare dashi shekara 8, inaso ya ara mani kudi harma nace mu rubuta agreement ni da shi zan dinga biyanshi kadan kadan tunda muna aiki tare, amma ko da yaushe yana yi man wasa da hankali kuma bawai kudin ke babu ba, Malam ga nauyin iyalai akaina. malam ataimaka da shawara.
nagode.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullah wa barakatuh. Babu laifi idan kana da wasu Bukaty kace ma wani abokinka ko kuma wani Salihun bawan Allah ya RAYAKA wajen yin addu'a domin cimma bukatarka ta alkhairi.
Amma babban abinda ake tsoro shine kar kaje wajen wani wanda zai umurceka dash yin shirka ko kuma wani mummunan abu domin samun biyan bukatarka.
Shi kuwa Ubangidan naka, ya dace ya taimaka maka. Tunda yin hakan yana daga cikin ayyukan da zai samu lada domin su. Kuma UBANGIJI ma yana zargin mutanen da suke Qin bayar da taimako.
Kaci gaba da neman bukatarka awajen Allah. Idan Allahn yaso sai ka samu abun nemanka awajen Ubangidan naka ko kuma ta wata hanya wacce tafi alkhairi gareka.
WALLAHU A'ALAM.