Assalamu Alaikum Malam Don Girman Allah Ka Taimaka Min Da Abinda Yake Damuna Ina Karatu A Jami'a Amma Malam Innayi Karatu Baya Shiga Kuma Ina Fama Da Yawan Mafarke Mafarke Sai Naji An Danne Ni Da Kyar Da Addua Abin Zai Sakeni Inna Tashi Da Safe Kuma Sai Ciwon Kai Da Ciwon Jiki Kuma Baifi Kwana Uku Ba Sai Naji A Mafarki Wai Kar Naga Basu Zo ba Wai Sunyi Tafiya Ne.
Don Girman Allah Malam Ka Taimaka Ina Cikin Wani Hali A Boye Sunana.
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullah wa barakatuh.
Wadannan Mishkilolin da kika lissafa duk suna daga cikin manyan alamomin jinyar da ta shafi SHAFAR ALJANU. Amma shawarwarin da zan baki sune kamar haka:
1. Ki yawaita karatun Alqur'ani da zikirin Allah safiya da maraice. Kuma ki rika zama da alwala ko yaushe.
2. Ki kula sosai da Zikirorin neman tsari irin wadannan da Sunnar Manzon Allah (saww) ta karantar damu.
3. Ki nisanci duk wani nau'in sabon Allah afili da boye.
4. Ki Yawaita sauraron karatun Alqur'ani acikin wayarki. Ku nisanci sauraron kida da waka.
5. Ki rike ayatul kursiyyi sosai. Ki yawaita yinta. Musamman idan zaki kwanta barci kiyi alwala ki karanta AYATUL KURSIYYI din tare da Aamanar Rasulu da Qul huwallahu da falaki da naasi Qafa uku uku.
6. Ki nemi magungunan ZAUREN FIQHU Kamar irin su Almujarrab, MUHRIKUL JINNI, Brain Tonic, da sauransu.
Idan kina bukata zaki iya tuntubar Saliha Wada Inuwa Zaria, ko kuma Babangida akan lambar wayar nan 08163621213.
Allah ya sawwake. Allah shi baki lafiya.
WALLAHU A'ALAM.