Dakarun Najeriya sun hallaka mayakan Boko Haram da dama tare da kwato makamai da kayayyakin hada Bam a jihohin Borno da Yobe a wannan mako.
Rundunar Sojojn Najeriya ta bayyana cewa dakarunta sun samu nasarar hallaka mayakan Boko Haram da dama tare da kwato makamai da kayayyakin hada bama-bamai a jihohin Borno da Yobe a wata fafatawa da suka yi a ranar Alhamis.
Sanarwar da rundunar Sojojin ta fitar wanda kakakinta Kanar Sani Kuka Sheka ya rattabawa hannu ta kuma bayyana cewa dakarun sun samu nasarar kame wasu mutane da ake zargin su ne ke samar da man fetur da abinci ga mayakan kungiyar.
Nasarar sojin Najeriya kan Boko haram
An kuma nuna wasu hotuna na irin kayayyakin da rundunar ta ce ta kwato daga mayakan, ciki har da wasu dabbobi da kuma makamai da kayayakin hada bama-bamai da hotunan wasu mutane da aka bayyana cewa daya Mai Mustapha shi ne ke samar da man fetur da wani mai suna Modu da aka ce shi ne ke samar da kayan abinci ga mayakan Boko Haram.
Akwai yiwuwar an fitar da wadan nan hotuna ne don gamsar da jama’a irin nasarorin da ake ikirarin Sojojin na samu saboda kawar da shakku a zukatan al’umma ganin yadda a baya ake tababar abubuwan da jami’an tsaron ke bayyanawa.
Ci gaban hare-haren BokoHaram
A ‘yan kwanakin nan dai rundunar sojojin Najeriya na ayyana samun nasara a yaki da Kungiyar Boko Haram sai dai kuma mayakan kungiyar na ci gaba da kai hare-hare a wasu sassan jihohin Borno da Yobe tare da hallaka mutane da dama.
Ko a ranar Alhamis wani farmaki da ‘yan kungiyar suka kai a wasu kauyuka a jihar Yobe ya haifar da mutuwar mutane 9 inda kuma suka kwashe kayakkin tare da kona gidaje da dama bayan wanda aka hallaka wasu masunta a tsakanin Gamboru da Baga a jihar Borno.
Wannan yasa wasu ke nuna damuwa ga kwan gaba kwan baya da ake samu a wannan yaki.
Malam Bala Kali Gaya wani ne daga cikin al’ummar yankin Arewa maso gabashin Najeriya ya bayyana daurewar kai kan yadda ake bayyana samun nasara, amma kuma mayakan na ci gaba da hallaka jama’a.
Sai dai ga Abubakar Abdullahi wani mai fashin baki kan harkokin tsaro, sojojin na samun nasara kuma sai a hankali za a iya fahimtar nasarar da ake samu a wannan yaki.
Jami’an tsaron dai na kara jaddada kira ga jama’a cewar aikin tabbatar da tsaro na kowa da kowa ne abinda ya sa Hamza Umar Usaman ya shawarci al’umma kamar da su bada hadin kansu ga jami'an tsaron a cikin wannan aiki.
Masana tsaro dai na kara bayyana bukatar hawa teburin shawara don kawo karshen rikicin tunda gwamnatin ta nuna akwai yiwuwar haka.
Title :
Sojin Najeriya na kara samun nasara kan Boko Haram
Description : Dakarun Najeriya sun hallaka mayakan Boko Haram da dama tare da kwato makamai da kayayyakin hada Bam a jihohin Borno da Yobe a wannan mako. ...
Rating :
5