Shugaba Buhari ya kuma maido da tsohon manajin darekta na hukumar tasoshin jiragen ruwan Najeriya, Habibu Abdullahi, a kan wannan mukamin da tun farko aka cire shi
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya kori manajin darekta na Hukumar Tasoshin Jiragen Ruwan Najeriya, Alhaji Sanusi Ado Bayero, daga kan mukaminsa.
Wata sanarwar da mai ba shugaba Buhari shawara kan yada labarai, Femi Adesina, ya bayar, ta ce wannan korar ta fara aiki nan take.
An umurci Alhaji Sanusi Ado Bayero da ya mika ragamar jagorancin hukumar ta NPA da kuma dukkan kayan gwamnati dake hannunsa ga Malam Habibu Abdullahi, wanda shugaba Buhari ya sake mayarwa kan wannan kujera ta manajin darekta na hukumar NPA a bayan da aka saukar da shi a baya.
Title :
Shugaba Buhari Ya Saukar Da Sanusi Ado Bayero Daga Mukaminsa
Description : Shugaba Buhari ya kuma maido da tsohon manajin darekta na hukumar tasoshin jiragen ruwan Najeriya, Habibu Abdullahi, a kan wannan mukamin da...
Rating :
5