Assalamu alaikum Malam tambayata itace shin Musulmai ma zasu shiga Wuta? Kuma shin dukkan musulmin da ya shiga wuta zai dauwama ne acikinta?
(Daga Abubakar Sani Jos)
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullah wa barakatuh. Bisa Sahihiyar Aqeedah ta Ahlus Sunnah Wal Jamaa'ah, Lallai akwai Musulmai masu sabon Allah wadanda zasu shiga wuta idan har sun mutu basu tuba ba.
To amma Annabi (saww) zau ceci wasu tun kafin asanyasu a wutar. Wasu kuma sai bayan sun shiga wutar sun sha wahala sannan a fiddasu.
Babu wani musulmi wani wanda zai dawwama a wuta. Kafirai ne masu dawwama acikinta.
WALLAHU A'ALAM.